Home Back

Ta yaya za a kwatanta ƙarfin Iran da na Isra'ila?

bbc.com 2024/5/10
Iran's Supreme Leader, Ali Khamenei and Israel's Prime Minister, Benjamin Netnayahu, with images of toy soldiers fighting

Asalin hoton, Getty Images

  • Marubuci,
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Urdu & BBC News Persian
  • Mintuna 15 da suka wuce

Hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka da Iran ta fara kai wa Isra'ila ranar Asabar 13 ga watan Afrilu sun kara sanya fargabar dagula al'amura a yankin Gabas ta Tsakiya.

Duk da cewa ba a samu asarar rayuka masu yawa a Isra'ila ba, hare-haren abubuwan fashewar fiye da 300 sun nuna irin ƙarfin da Iran ke da shi na iya harba makamai daga nesa.

Lamarin ya kasance wani babban abin da aka daɗe ana fargabar faruwarsa na rikici a yankin, baya ga hare-haren da wasu ƙungiyoyi ƙawayen Iran ke kai wa Isra'ila, da kuma hare-haren da ake kai wa ƙawayen Iran da ake zargin Isra'ila da aikatawa.

A yanzu haka Isra'ila na yaƙi a Gaza, haka kuma tana samun ƙaruwar fuskantar yaƙi da ƙungiyar Hezbollah a kan iyakarta da Lebanon, don haka fara wani yaƙin ka iya haifar da wata matsalar.

Babban hafsan sojin Isra'ila Laftanar Kanal Herzei Halevi ya ce ƙasarsa za ta mayar da martani game da harin na ranar Asabar, sai dai bai yi ƙarin bayani ba.

Haka shi ma mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Ali Bagheri Kani, ya shaida wa gidan talbijin na ƙasar cewa ƙasarsa za ta mayar da martani game da harin Isra'ila cikin daƙiƙoƙi, ba sai sa'o'i ba.

Asalin hoton, Getty Images

Iranian missiles on display
Bayanan hoto, Ƙarfin makamai masu linzami da Iran ke da shi na daga cikin ƙarfin sojinta

Wacce ƙasa ce ta fi ƙarfi?

BBC ta duba wannan tambaya ta hanyar amfani da wasu kafofi da aka lissafa a ƙasa, duk da cewa kowace ƙasa na da fannin da ta fi ƙarfi.

Cibiyar Nazarin Dabarun Yaƙi ta Duniya (IISS) ta duba ƙarfin sojin ƙasashen biyu, ta hanyar amfani da alƙaluman hukumomi da abin da ake gani a ƙasa wajen ƙiyasta ƙarfin ƙasashen.

Haka kuma wasu ƙungiyoyi kamar Cibiyar Binciken Zaman Lafiya ta Stockholm, ita ma ta duba wannan batu, sai dai alƙaluman kan bambanta ga ƙasashen da ba su bayar da alƙaluma ba.

Haka ma, Nicholas Marsh daga cibiyar Binciken zaman lafiya ta Oslo (PRIO), ya ce ana kallon IISS a matsayin wadda ke auna ƙarfin sojin ƙasashen duniya.

Israel and Iran's population, Gross Domestic Product (GDP), defence budget and defence as a proportion of GDP (4% for israel and 2% for Iran)

IISS ta ce Isra'ila na zuba kuɗaɗe masu yawa a fannin tsaro a kasafin kuɗinta fiye da Iran, lamarin da ya sa take samun ƙarfi a kowane yaƙi da take yi.

IISS ta ce a shekarar 2022 da 2023, Iran ta zuba kusan dala biliyan 7.4 a fanin tsaro a kasafin kuɗinta, yayin da Isra'ila ta zuba kusan dala biliyan 19.

Don haka kudin da Isra'ila ke kashewa a fannin tsaronta idan aka kwatanta da arzikin cikin gida da ƙasar ke samu (GDP) ya ninka na Iran.

Asalin hoton, Getty Images

Jirgin F-35
Bayanan hoto, Jirgin F-35 na ɗaya daga cikin manyan jiragen saman yaƙi na duniya

Ƙarfin fasaha

Alƙaluman IISS sun nuna cewa Isra'ila na da jiragen yaƙi 340, lamarin da ke ba ta damar kai hare-hare ta sama.

Daga ciki akwai F-15 wanda ke harba makami mai dogon zango, da kuma jiragen F-35 da ke da ƙarfin hari tare da kai wa jirage masu saukar ungulu hari.

Haka nan IISS ta ƙiyasta cewa tana da jiragen yaƙi kusan 320. Tana da jiragen tun shekarun 1960 ciki har da F-4 da F-5 da kuma F-14 - wanda ya yi fice a shekarar 1986.

Amma Nicholas Marsh na cibiyar PRIO ya ce ba a san ko har yanzu tsoffin jiragen na tashi ba, saboda kayan gyaransu na wahalar samu.

Asalin hoton, Getty Images

Sojojin Ruwan Amurka ne suka fara amfani da jirgin F-14, shekara 20 da suka gabata amma har yanzu ana aiki da shi a Iran
Bayanan hoto, Sojojin Ruwan Amurka ne suka fara amfani da jirgin F-14, shekara 20 da suka gabata amma har yanzu ana aiki da shi a Iran

Na'urar kakkaɓo makamai masu linzami

Na'urorin kakkaɓo makamai masu linzami su ne ƙashin bayan tsaron Isra'ila.

Injiniyan makami mai linzami, Uzi Robin ne ya samar da na'urar kakkabo makamai masu linzami a ma'aikatar tsaron ƙasar.

A yanzu shi ne babban mai bincike a cibiyar nazarin dabarun tsaro a Birnin Kudus, ya kuma shaida wa BBC yadda ya ji ya samu ''kariya'' a lokacin da na'urorin suka kakkaɓo makamai masu linzami da jirage masa matuƙa da Iran ta harba wa Isra'ila ranar Asabar.

"Na samu gamsuwa, na kuma yi murna, na'urorin na ƙoƙarin kakkaɓo makamai''

Asalin hoton, Amir Cohen / Reuters

Na'urorin kakkaɓo makamai na Isra'ila sun lalata fiye da makamai masu linzami 300 da jirage marasa matuƙa da Iran ta harba a makon da muke ciki.
Bayanan hoto, Na'urorin kakkaɓo makamai na Isra'ila sun lalata fiye da makamai masu linzami 300 da jirage marasa matuƙa da Iran ta harba a makon da muke ciki.

Nisan da ke tsakanin Iran da Isra'ila

Isra'ila na da nisan fiye da kilomita 2,100 daga Iran. Makamanta masu linzami na daidai wurin da za ta harba wa ƙasar, kamar yadda editan hukumar tsaron ƙasar Tim Ripley ya shaida wa BBC.

Tasawirar Iran da Isra'ila

Ana kallon shirin makamai masu linzami na Iran a matsayin wanda ya fi girma tare da faɗi a yankin Gabas ta Tsakiya.

A shekarar 2022, Janar Kenneth McKenzi na Hukumar tsaron Amurka, ya ce Iran na da makamai masu linzami fiye da 3,000.

Haka ma cibiyar kula da tsaron makamai masu linzami ta CSIS, ta ce Isra'ila na sayar wa wasu ƙasashen duniya makamai masu linzami.

Asalin hoton, EPA

Iranian missile or drone fired at Israel
Bayanan hoto, Iran ta harba makamai masu linzami fiye da 300 da jirage marasa matuƙa zuwa Isra'ila a ranar Asabar 13 ga watan Afrilu

Makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa na Iran

Iran ta fara babban aikin ƙera makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa tun bayan yaƙin da ta yi da makwabtanta daga shekarar 1980 zuwa 1988.

Ta kuma ƙera makamai masu cin gajere da dogon zango da kuma jirage marasa matuƙa, waɗanda da yawansu yanzu ta harba wa Isra'ila.

Masu nazari sun ce a Iran ne aka ƙera makamai masu linzami da 'yan tawayen Houthi suka harba wa Saudiyya.

Asalin hoton, Reuters

Iranian consulate building in rubble
Bayanan hoto, An lalata ginin ofishin jakadancin Iran a Syria a wani hari ta sama da aka kai ranar 1 ga watan Afrilu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani babban jami'in sojin Iran

Hari da makamai masu cin dogon zango

Tim Ripley ya ce ba lallai ne Isra'ila ta iya yaƙin ƙasa da Iran ba.

"Babbar damar da Isra'ila ke da ita ita ce ƙarfin sama da kuma tarin makamai da ake amfani da su ta sama, don haka tana da damar kai hari ta sama zuwa duka wuraren da take da niyyar kai wa a Iran''.

Mista Ripley ya ce Isra'ila za ta iya kashe jami'ai tare da lalata rijiyoyin man Iran ta sama.

A baya an kashe manyan sojoji da manyan fararen hula a wasu hare-hare ta sama, ciki har da harin da aka kai wa ginin ofishin jakadancin Iran a Syria, wanda shi ne ya haddasa harin na Iran.

Isra'ila ba ta ɗauki alhakin harin ba da kuma sauran hare-haren da aka kai wa manyan jami'an Iran.

Sai dai ba ta musanta zarginta da kai harin ba.

Asalin hoton, IRGC handout / Reuters

Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) Navy's speedboats move during an exercise in Abu Musa Island, in this picture obtained on 2 August 2023
Bayanan hoto, Jiragen ruwan dakarun juyin juya halin Iran yayin da suke atisaye a tsibirin Abu Musa

Dakarun sojin ruwa

Rundunar sojin ruwan Iran na da kusan jiragen ruwa 220, yayin da Isra'ila ke da kusan 60, kamar yadda rahoton cibiyar IISS ya nuna.

Asalin hoton, EPA

A man paddles in front of a German-made Sa'ar 6-class corvette of the Israeli navy docked at the Red Sea port city of Eilat on 16 April 2024
Bayanan hoto, IISS ta ce Isra'ila na da jiragen sojin ruwa kusan 60

Asalin hoton, Iranian government / Getty Images

 The Iranian president in 2008, Mahmoud Ahmadinejad (centre) visits the Natanz uranium enrichment facilities on 8 April 2008 300 km south of Tehran -  Ahmadinejad announced on Iranian state television during the visit that Iran had begun the installation ofs6,000 new centrifuges, adding to to the 3,000 centrifuges already at the facility
Bayanan hoto, A shekarar 2008, shugaban Iran na wancan lokacin, Mahmoud Ahmadinejad, ya bayyana cewa an samu karuwar samar da makamashin uranium a tashar nukiliyarta da ke Natanz

Barazanar makamin nukiliya

Ana ɗaukar Isra'ila a matsayin wadda ta mallaki makamain nukiliya, amma tana ci gaba da ƙin bayyana hakan.

Amma ba a tunanin Iran ta mallaki makamin, duk da zarge-zargen mallakar makamin da ake yi mata, Iran ta musanta zargin cewa za ta yi amfani da makaminta na nukiliya, wanda ta ce na zaman lafiya ne don zama na yaƙi.

Girman ƙasashen da yawan al'ummominsu

Iran ta fi Isra'ila girman ƙasa da yawan al'umma, inda take da kimanin mutum miliyan 89, saɓanin Isra'ila mai kusan miliyan 10.

Haka kuma Iran ta ninka Isra'ila yawan sojojin da ke bakin aiki, inda take da sojoijin da ke bakin aiki kusan 600,000, yayin da Isra'ila ke da sojoji 170,000 kamar yadda IISS ta nuna.

Asalin hoton, Reuters

A ballistic missile with a man standing next to it - the missile is almost as wide as him
Bayanan hoto, Wani makami mai linzami da ya faɗi a tekun Dead Sea bayan da Iran ta ƙaddamar da harin makamai masu linzami da jirage mnarasa matuƙa ranar Asabar

Mene ne 'yaƙin Isra'ila da Iran'

Duk da cewa Isra'ila da Iran ba su taɓa yin yaƙi a hukumance tsakaninsu ba, ƙasashen sun sha yin sa-in-sa tare da nuna wa juna yatsa.

An sha kisan manyan jami'an Iran a wasu ƙasashe ta hanyar wasu hare-haren da ake ɗora alhakinsu kan Isra'ila, ciki har da Iran, yayin da ita kuma Iran ke kai hari zuwa cikin Isra'ila ta hanyar amfani da ƙawayenta.

Ƙungiyar Hezbollah da ke Lebanon ce ke yin mafi yawan yaƙin Iran kan Isra'ila daga Lebanon. Iran ba ta musanta mara wa Hezbollah baya ba.

Haka ma goyon bayan da take bai wa Hamas a Gaza. Hamas ta kai hare-haren 7 ga watan Oktoba kan Isra'ila tare da jefa makaman rokoki daga Gaza zuwa cikin Isra'ila na tsawon gomman sekaru.

Isra'ila da ƙasashen Yamma sun yi amanna cewa Iran na samar da harsasai da bindigogi da kuma horo ga maƙayan Hamas.

Asalin hoton, Houthi militants handout / EPA

Houthi fighters sitting around a flag
Bayanan hoto, Mayaƙan Houthi na kai hare-hare kan jiragen ruwa a Tekun Maliya

Ana kallon mayaƙan Houthi a Yemen a matsayin wata kafar da Iran ke amfani da ita. Saudiyya ta ce makaman da mayaƙan Houthi ke harba mata an ƙera su ne a Iran.

Ƙungiyar da ke samun goyon bayan Iran na da ƙarfi a Iraƙi da Syria. Haka nan, Iran na goyon bayan gwamnatin Syria, inda aka ce tana amfani da Syria wajen kai hari Isar'ila.