West Ham ta kammala ɗaukar Kilman
West Ham ta kammala ɗaukar ƙyaftin din Wolves, Max Kilman kan £40m kan yarjejeniyar kaka bakwai.
Mai tsaron bayan zai sake aiki karkashin Julen Lopetegui, wanda ya naɗa shi mukamin a lokacin da ya horar a ƙungiyar da ke Molineux.
Tun farko Wolves ba ta sallama tayin farko da West Ham ta yi na £25m ba, daga baya ta amince da na biyu kan ɗan wasan da ta ɗauka daga Maidenhead kan £40,000 a 2018.
Maidehead, wadda ke buga The National League za ta samu kaso 10 cikin 100 a cinikin da zai kai £4m.
Kilman ya buga wa Wolves wasa 151 da cin ƙwallo uku tun bayan da ya fara buga mata tamaula a Mayun 2029.
Ya zama na uku da West Ham ta saya a bana, bayan gola ɗan kasar Brazil, Wes Foderingham da kuma matashi daga Brazil, Luis Guilherme.
Lopetegui ɗan kasar Sifaniyya ya maye gurbin David Moyes, bayan kammala kakar da ta wuce.