Home Back

Emre Can ya maye gurbin Pavlovic a tawagar Jamus a Euro 2024

bbc.com 2024/8/21
Aleksandar Pavlovic

Asalin hoton, Getty Images

Wanda aka sabunta Minti 1 da ta wuce

An maye gurbin dan wasan Bayern Munich, Aleksandar Pavlovic da Emre Can a tawagar Jamus da za ta buga Euro 2024, sakamakon jinya.

Pavlovic, mai shekara 20 ya fara yi wa tawagar tamaula ranar 3 ga watan Yuni a wasan sada zumunta da Jamus ta yi canjaras da Ukraine.

Tuni kuma koci, Julian Nagelsmann ya gayyace shi cikin wadanda za su buga wa kasar gasar cin kofin nahiyar Turai da za a fara daga 14 ga watan Yuni.

Sai dai bai buga wa Jamus wasan sada zumunta da ta ci Girka 2-1 ranar Juma'a ba, tuni aka sanar da shi za a maye gurbinsa, bayan da yake fama da jinya.

Tuni kuma aka mika goron gayyata ga tsohon dan wasa Liverpool, Can wanda ya maye gurbinsa.

Can mai shekara 30 ya buga wa Jamus wasa 43, an kuma kira shi, maimakon dan kwallon Bayern Munich, Leon Goretzka, don maye gurbin Pavlovic.

Ranar Juma'a 14 ga watan Yuni Jamus za ta fara wasan farko a cikin rukuni da Scotland a Munich.

People are also reading