Home Back

Ana Batun Yarjejeniyar Samoa, Tinubu Ya Fadi Abin Kunyar da Najeriya Ta Yi

legit.ng 2024/10/5
  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya koka kan wutar lantarkin da ƙasar nan ke samarwa duk da girman da take da shi
  • Shugaba Tinubu ya bayyana cewa abin kunya ne a ce ƙasar abin da kawai take samarwa na wutar lantarki shi ne 4.5GW
  • Ya nuna cewa akwai buƙatar ƙara yawan wutar lantarkin da ake samawarwa da rarraba ta a faɗin ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwarsa kan ƙarancin wutar lantarkin da Najeriya ke samarwa.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa abin kunya ne duk girman Najeriya har yanzu wutar lantarki mai ƙarfin 4.5GW kawai take iya samarwa.

Tinubu ya damu kan wutar lantarki a Najeriya
Tinubu ya ce abin kunya ne Najeriya tana da samar da wutar lantarki 4.5GW Hoto: @DOlusegun Asali: UGC

Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da majalisar daidaita tattalin arziƙi (PECC), a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Tinubu ya ce kan tattalin arziƙi?

Shugaba Tinubu ya nuna muhimmancin yin amfani da sababbin dabaru domin magance ɗumbin matsalolin tattalin arziƙin da ƙasar nan ke fama da su, rahoton New Telegraph ya tabbatar.

"Muna da ƙalubalen tsaron makamashi a Najeriya. Ya kamata mu haɗa hannu wajen inganta harkar man fetur da iskar gas, haka nan kuma mu ƙara samar da wutar lantarki da rarraba ta a faɗin ƙasar nan."
"Mun ƙudiri aniyar yin hakan tare da haɗin kan ku, haɗin gwiwarku, da shawarwarinku. A matsayinmu na ƙasa, abin kunya ne har yanzu muna samar da wutar lantarki mai ƙarfin 4.5GW."
"Dole ne mu ƙara yawan man da muke haƙowa zuwa ganga miliyan biyu a kowace rana a cikin ƴan watanni masu zuwa, kuma mun ƙudiri aniyar kawar da duk wani ƙalubale da ke hana saka hannun jari a ɓangaren makamashi tare da ƙarfafa yin gasa."

- Bola Tinubu

Malaman addini sun caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa malaman addinin musulunci da-dama sun fito sun yi magana bayan jin labarin Najeriya ta shiga yarjejeniyar Samoa.

Malaman addinin musuluncin waɗanda suka gabatar da huɗubobi a garuruwa daban-daban sun nuna ba za su goyi bayan alaƙar jinsi ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading