Home Back

Abubuwa 5 Da Sabuwar Dokar Masarautar Jihar Kano Ta Ƙunsa

premiumtimesng.com 2024/6/18
Kano State Assembly
Kano State Assembly

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa sabuwar doka, wadda ta maida fasalin masarautar jihar kamar yadda take kafin Gwamnatin Ganduje ta datsa masarautar gida biyar a cikin 2019.

Gyare-gyaren su na cikin Sabuwar Dokar Masarautar Kano ta 2024 (1445 A.H).

1. Soke Dokokin Da Gwamnatin Baya Ta Yi:
Wannan sabuwar doka ta soke Dokar Masarautun Jihar Kano na 2019, da duk wasu gyare-gyare da aka yi mata daga baya.

Hakan ya na nufin an rushe dokar da ta samar da sabbin masarautu 5 a Jihar Kano.

2. Rushe Masarautun Kano 5 Da Aka Ƙirƙiro Cikin 2019:

Wannan doka ta rushe masarautu 5 da aka ƙirƙiro cikin 2019, kuma duk muƙamai da aka ƙirƙiro na sarauta bayan dokar, su ma an rushe su.

Duk wani naɗi da ƙarin girman da aka yi wa wani mai riƙe da sarautar gargajiya bayan 2019, an rushe su.

3. An Dawo Da Dukkan Sarautun Da Dokar 2019 Ta Rushe:

Duk wani da aka bai wa wani muƙami a ƙarƙashin dokar 2019, to ya koma kan wancan muƙami na sa.

Hakan an yi ne domin a dawo da martabar al’adu da masarautar Kano.

4. Ƙarfin Ikon Gwamna Kan Masarautar Kano:
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bai wa Gwamna ƙarfin ikon ɗaukar duk wasu matakai da suka dace domin maida masarautar Kano kamar yadda take kafin dokar 2019.

Hakan ya na nufin har da ƙarfin ikon maida masu muƙamai kan muƙamin su na baya kafin kafa dokar harigido ta 2019.

5. Kwamishinan Ƙananan Hukumomi Zai Kula Da Masarautu:

An ɗora wa Kwamishinan Ƙananan Hukumomi kula da masarautu har zuwa lokacin sake naɗe-naɗe.

Kuma zai kula da kadarorin masarautu domin tabbatar da an koma kan turbar mulki wanda ake a kai kafin a yi amfani da dokar 2019 a baddala al’amurra.

People are also reading