Home Back

Gwamnatin Kano ta Ware N1bn Domin Muhimman Ayyuka a Bangaren Lafiya

legit.ng 2024/7/4
  • Gwamnatin Kano ta bayyana shirinta na farfado da harkokin lafiya domin inganta lafiyar al'ummar jihar tun daga daga bayar da magunguna kyauta
  • Wannan ya sanya majalisar zartarwar jihar amince da ware N1bn domin ba gwamna Abba Kabir Yusuf ikon aiwatar da aikace-aikacen da za su inganta harkokin lafiya a Kano
  • Sanarwar da daraktan yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta nuna za a sayo kayan haihuwa domin rabawa kyauta a asibitoci da ma inganta ilimin jinya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta amince da fitar da N1bn domin gudanar da wasu manyan ayyuka da za su taimaka wajen ci gaban harkar lafiya a jihar.

Wannan wani mataki ne na ganin cewa al'ummar Kano sun samu ingantaccen kiwon lafiya, musamman a asibitoci mallakin gwamnatin jihar.

Abba Kabir
Gwamnatin Kano ta ware makudan kudi domin ayyukan lafiya Hoto: Sanusi Bature Dawakin Tofa Asali: Facebook

A sanarwar da daraktan yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook, majalisar zartarwar jihar ce ta amince da fitar da kudin a zamanta na 15.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanne ayyuka za a gudanar?

Daga cikin ayyukan da gwamnati za ta gudanar da N1bn akwai sayo kayan haihuwa da ake rabawa kyauta a asibitoci kan N165m, kamar yadda 247ureports ta wallafa.

Sai N57m na sake bayar da kwangilar gina asibitin koyon aikin jinya da ungozoma a Madobi domin inganta ilimin dalibai a bangaren.

An ware N61.8m domin kammala asibitin Kadawa a karamar hukumar Gwale, N81.6m kuma an ware domin gina bangaren kula da masu cutar amosanin jini a asibitin kwararru na Murtala.

Za a yi amfani da N17.4m domin gyara cibiyar kebance masu dauke da cutuka masu yaduwa ta 'yar gaya, N770m domin gina cibiyar ungozoma a Gezawa.

N28.5m aka ware domin gyara kwalejin koyon aikin jinya da Ungozoma a Dambatta.

Gwamnatin Kano ta yi gargadi kan Kwalara

A baya kun ji cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta gargadi mazauna Jihar Kano kan bullar cutar amai da gudawa da aka fi sani da kwalara, tare da bayyana matakan kariya.

Kwamishinan lafiya a jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya yi gargadin, kuma daga matakan da ya bayar akwai lura da ta'ammali da ruwan sama da tsaftace kayan abinci.

Asali: Legit.ng

People are also reading