Home Back

KIBIYAR AJALI: Yadda Jami’in EFCC ya kashe kan sa a Abuja

premiumtimesng.com 3 days ago
YAƘI DA RASHAWA, ZAMBA DA ƁARAYIN GWAMNATI A 2022: EFCC ta maka mutum 3,785 kotu, ta yi nasara kan mutum 3,744

Wani jami’in Hukumar EFCC ya kashe kan sa, a gidan sa da ke Abuja, a ranar Litinin.

Mamacin dai ya rasu ne a mutuwar da ake zargin ya kashe kan sa ne da kan sa. PR Nigeria ta ruwaito labarin cewa babu wani cikakken bayani tukunna, amma EFCC da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya sun fara bincike.

Haka kuma PUNCH ta ruwaito cewa mamacin bai daɗe da komawa aiki ba daga wani hutu da ya ɗauka.

“Sai dai kuma lokacin da ya dawo aiki, mun lura da cewa ya rame sosai.”

Ana nan dai ‘yan sanda sun fara bincike domin gano musabbabin mutuwar ta sa.

Kakakin EFCC Wilson Uwujaren ya tabbatar da labarin mutuwar jami’in na su, sai dai ya ce su na jiran sakamakon binciken musabbabin mutuwar daga Rundunar ‘Yan Sanda.

People are also reading