Home Back

Yadda Aka Yi Bikin Kaddamar Da Littafin Babban Editan LEADERSHIP A Abuja

leadership.ng 4 days ago
Yadda Aka Yi Bikin Kaddamar Da Littafin Babban Editan LEADERSHIP A Abuja

A ranar Larabar nan ne aka kaddamar da wani mashahurin littafi da Babban Edita kuma Babban Mataimakin Shugaban Rukunin Kamfanonin LEADERSHIP, Mista Azubuike Ishiekwene ne ya rubuta, mai taken “Rubutu don Kafafan Yada Labarai da mayar da shin a kudi”.

Taron ya gudana ne a babbar cibiyar tunawa da Shehu Musa ‘Yar’Aduwa da ke tsakiyar Babban Birnin Tarayya Abuja.

Da yake gabatar da jawabi, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mo-hammad Idris, ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta himmatu wajen tal-lafa wa aikin jarida bisa ‘yanci.

Idris wanda yake magana a matsayin shugaban taron ya bayyana cewa, ““Yayin da muke murnar wannan gagarumin buki, yana da kyau mu sake jaddada aniyar gwamna-tin Tinubu na samar da ‘yancin aikin jarida.

“Mun fahimci cewa al’umma za ta ci gaba ne kawai idan sassanta na kafafen yada laba-rai suka sami ‘yancin bayar da rahoton gaskiya ba tare da fargabar ladabtarwa ba, san-nan kuma ta rika hukunta masu rike da madafun iko,” inji Idris.

Ya yaba wa Ishiekwene a matsayin marubuci, edita, shugaban gudanarwa, mawallafi, mai ba da shawara, kuma abin koyi, inda ya bayyana matsayinsa na Babban Ma-taimakin Shugaban Rukunin Yada Labarai na LEADERSHIP a matsayin abin jinjina.

Idris ya yaba da littafin, inda ya bayyana shi a matsayin wani tsari na kasuwanci wanda ke cike gibin da ke tsakanin aiki da kasuwanci a bangaren yada labarai.

Ya lura cewa littafin yana da amfani ga masu karatu da yawa, ciki har da matasa da manya, masu zaman kansu, ko kuma masu cikakken aikin jarida.

Idris ya kuma yaba wa Ishiekwene bisa yadda ya tara fitattun jaruman kafafen yada lab-arai, mawallafa, editoci, malamai, da ‘yan jarida domin kaddamar da littafin.

Ministan ya kara da bayyana Ishiekwene a matsayin shugaba wanda ya jagoranci man-yan gidajen yada labarai da horar da matasa kwararru.

Ya jaddada cewa babban sha’awar Ishiekwene ya kasance a cikin rubutu, inda yake tsara bayanai na fahimta ga jama’a cikin haske sama da shekaru talatin.

Idris ya bayyana muhimmancin ‘yan jarida a matsayin ginshikin tsarin dimokuradiyya, yana mai jaddada cewa al’umma na samun bunkasuwa yayin da kafafen yada labaranta za su iya bayar da labarin gaskiya ba tare da tsoro ba tare da dora wa masu rike da ma-dafun iko alhakinsu na kula da jama’a.

Ita ma a nata bangaren, Shugabar Rukunin Kamfanonin LEADERSHIP, Zainab Nda-Isaiah, ta bayyana damuwarta kan yadda `yan jarida da marubuta ke fama da kamfar kudi da sukuni, duk kuwa da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen fito da ra’ayin jama’a da kawo sauyi a cikin al’umma.

Da take jawabi a wajen taron, ta jaddada rashin jin dadin halin da marubuta da yawa suke fuskanta na talauci duk da ayyukan da suke yi masu muhimmanci.

Ta yi imanin cewa littafin Ishiekwene zai ba da haske mai mahimmanci da kuma koyar aiki don taimakawa marubuta su guje wa cusa kai cikin duhu da wahalar samun kudi.

Zainab ta bayyana littafin a matsayin cikakken jagora wanda ba wai kawai ya shafi tsarin rubuce-rubuce ne ba har ma da jan hankali kan amfani da fasahar rubuce-rubuce wajen samun kudade.

Ta kuma yaba wa babban editan kuma babban mataimakin shugaban kamfanin LEADERSHIP Ishiekwene bisa jajircewarsa da sanin ya kamata, wanda hakan ya taimaka matuka wajen ci gaban littafin.

Da yake jawabin godiya, Mista Azubuike Ishiekwene ya nuna jin dadinsa bisa yadda aka amsa goron gayyatar bikin tare da jaddada cewa godiyarsa ba za ta misaltu ba.

Taron ya samu halartar manyan mutane irin su Sanata Ireti Heebah Kingibe, da mawallafin jaridaer Ban-guard Sam Amuka, da Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo, SAN, da tsohon kakakin shugaban kasa Dr. Reuben Abati, fitaccen marubucin jarida kuma mai gabatar da shirye-shiryen talabijin.

People are also reading