Wike Na Cikin Alheri Dumu Dumu: Majalisa Ta Amince da Karin N98.5bn Ga Kasafin Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
FCT, Abuja - Majalisar dattijai ta amince da karin Naira biliyan 98.5 a kasafin shekarar 2024 na ma'aikatar kula da babban birnin tarayya, Abuja.
Jaridar This Day ta ce a makon da ya gabata majalisar wakilai ta fara amince wa da kudurin dokar gabanin gabatar da shi ga majalisar dattawan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya bayyana amincewa da kudurin karin kudin a zaman majalisar na yau, kamar yadda rahoton Channels ya nuna.
Majalisar ta amince da kudirin dokar ne bayan duba rahoton da kwamitin ta na babban birnin tarayya ya gabatar mata kan karin kasafin kudin.
Kafin amincewa da rahoton, Seata Ireti Kingibe, ta gabatar da wani korafi na cewa an yi watsi da ita a ayyukan kwamitin na babban birnin tarayya duk da ta kasance mamba a ciki.
Shugaban majalisar dattawan ya duba korafin nata inda ya ba ta shawarar da ta bi ka’ida, ta hanyar rubuta kokenta da gabatar shi a gaban majalisar a matsayin kudiri.
Legit Hausa ta ruwaito cewa a kwanakin baya ne shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar da kudirin karin kasafin kudin birnin tarayyar a gaban majalisar tarayyar.
Tinubu ya tunatar da ‘yan majalisar cewa ana bukatar kudin ne domin gudanar da muhimman ayyukan more rayuwa a babban birnin kasar wanda ba ya a cikin kasafin na farko.
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan majalisar wakilai sun gabatar da kuduri da zai taikata wa'adin shugaban kasa da gwamnoni zuwa shekara 6 babu tazarce.
Haka zalika kudurin na neman a kirkiri karin ofishin mataimakin shugaban kasa ta yadda shiyyoyin Arewa da Kudu za su zamo suna da kujerar mataimaki.
Asali: Legit.ng