Home Back

Jirgin Kashim Shettima ya kakare, ya kasa kai shi Amurka taron da zai wakilci Tinubu

premiumtimesng.com 2024/5/19
Jirgin Kashim Shettima ya kakare, ya kasa kai shi Amurka taron da zai wakilci Tinubu

Ɗaya daga cikin jirgin da ke Bargar Jiragen Shugaban Ƙasa, ya kakare, yadda hakan ta sa ya kasa tashi saboda wasu matsaloli. Lamarin dai ya kai ga Mataimakin Shugaban Ƙasa ya soke ziyarar da ya shirya kaiwa Amurka, domin ya wakilci Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu wani taron Inganta Tattalin Arziki Tsakanin Amurka da Afrika.

Kakakin Yaɗa Labaran Kashim Shettima, Stanley Nkwocha, ya bayyana a ranar Litinin cewa a yanzu dai Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar ne zai wakilci Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a wurin taron.

Dama dai a ranar Lahadi Nkwocha ya ce Mataimakin Shugaban Ƙasa zai tashi zuwa Amurka a birnin Dallas, Texas, domin ya wakilci Shugaban Ƙasa, wanda shi ma fiye da sati ɗaya ba ya cikin Najeriya.

Sanarwar ta ce idan ya je zai yi jawabi ne kuma zai jagoranci wani zaman tattaunawa da masu sha’awar zuba jari a Najeriya.

To sai dai a ranar Litinin kuma Nkwocha ya ce Shettima ba zai samu halartar taron ba, saboda jirgin da zai ɗauke shi ya samu matsala.

Ya ce masu kula da Bargar Jiragen Shugaban Ƙasa ne suka ba shi shawarar fasa tafiyar. Ya ce amma yanzu an tsara cewa Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar ne zai wakilci Shugaba Tinubu a wurin taron.

People are also reading