Tinubu Ya Ba Da Umarnin Lallai A Kamo Makasan Dutsinma da Kankara A Katsina
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su bibiyi tare da kamo maharan da ke da alhakin kai hare-haren baya-bayan nan a ƙananan hukumomin Dutsin-Ma da Ƙanƙara na jihar Katsina.
Shugaban ya yi Allah-wadai da waɗannan hare-hare, inda ya kira su da mugun nufi, sannan ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da tsaron ƴan kasa da kuma kawar da ƴan ta’adda.
Tinubu, ta bakin mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya jajantawa iyalan mamatan da al’ummar jihar Katsina, yana mai addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasa rayukansu. Ya kuma ba da tabbacin za a zage damtse wajen ganin an gurfanar da masu laifin a gaban kuliya da kuma inganta tsaro a faɗin ƙasar nan.
Hare-haren da aka kai a Yargoje da Kankara a ranakun 9 da 10 ga watan Yuni sun yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 25, inda har yanzu ba a san ko su waye ba.
Wannan ta’addancin ya biyo bayan hare-haren da aka kai tun farko a ƙananan hukumomin Dutsin-Ma da Safana a tsakanin ranakun 4 zuwa 6 ga watan Yuni, inda wasu gungun ‘yan bindiga suka kashe aƙalla fararen hula 30.