Home Back

Bello Matawalle Ya Tona 'Yan Arewan da ke Kokarin Ganin Bayan Tinubu a Zaben 2027

legit.ng 2 days ago
  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana nau'in yan Arewa da suke ƙoƙarin ganin ƙarshen mulkin Bola Tinubu
  • Alhaji Bello Matawalle ya ce kokarin kayar da shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 ba abu bane da ya kamata ya fito daga yankin Arewa
  • Har ila yau, tsohon gwamnan ya fadi ayyukan alheri da shugaba Bola Tinubu ya yi a Arewa wanda ya kamata a kara zabensa saboda su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma ministan tsaro, Bello Matawalle ya koka kan masu kokarin kayar da Bola Tinubu a 2027.

Bello Matawalle ya ce Bola Tinubu ya yi abubuwan alheri a Arewacin Najeriya wanda ya kamata a saka masa da ƙara zaɓensa karo na biyu.

Bello Matawalle
Bello Matawalle ya bukaci a cigaba da goyon bayan Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu|Bello Matawalle Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon gwamnan ya ce kokarin kayar da Tinubu a 2027 ba zai kai ga nasara ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu kokarin kayar da Tinubu a 2027

Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya ce yan siyasa masu nuna bani-na-iya ne masu son juyawa Bola Tinubu baya a Arewa.

Bello Matawalle ya kara da cewa wasu daga cikinsu kuma ba su da magoya baya amma a haka suke ganin za su iya kayar da Bola Tinubu a 2027.

Alherin da Tinubu ya yi a Arewa

Bello Matawalle ya bayyana cewa Bola Tinubu ya ja yan Arewa a jiki cikin mulkinsa inda ya ba su manyan mukamai, rahoton Leadership.

Tsohon gwamnan ya ce Bola Tinubu ya mikawa yan Arewa ragamar tsaro inda ya basu ministocin tsaro da mai ba shi shawara kan tsaro da sauran manyan mukamai.

Matawalle: 'Mu goyi bayan Tinubu'

A karshe, Bello Matawalle ya yi kira ga yan Arewa a kan su cigaba da goyon bayan gwamnatin shugaba Tinubu wajen inganta tattalin Najeriya.

Masana na ganin cewa Bello Matawalle ya yi martanin ne biyo bayan magana da Lukman Salihu ya yi kan cewa Bola Tinubu ya gaza tabuka komai ga yan Arewa.

Matawalle ya wanke kansa daga zargi

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Bello Matawalle ya kare kansa daga zarge-zargen da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ke yi masa.

Gwamna Dauda ya na zargin Matawalle da sama da fadi da makudan kudaden jihar da kuma wasu laifukan da suka shafi rashawa.

Asali: Legit.ng

People are also reading