Home Back

Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan ƙarin kuɗin lantarki

bbc.com 2024/5/18
...

Asalin hoton, Getty Images

  • Marubuci, Aisha Babangida
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
  • Aiko rahoto daga Abuja

Tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da ƙarin kuɗin wutar lantarki ga masu samun wutar lantarki ta tsawon sa'o'i 20 a kullum waɗanda suke ajin A kenan, 'yan kasar na ci gaba da nuna damuwa da korafe-korafe da kuma tambayoyi kan lamari.

Wannan matakin dai ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriyar ke kokawa kan mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki da kuma tsadar rayuwa.

A ranar Laraban da ta gabata ne hukumar da ke kula da wutar lantarkin a Najeriyar ta sanar da sabon farashin da abokan huldarsu za su fara biya.

Hukumar ta ce kwastomomi za su fara biyan naira 225 a kan kowane ma'auni daya na wutar (unit) inda a baya suke biyan N66.

'Yan Najeriya da dama, waɗanda tuni suke fama da ƙalubalen tsadar rayuwa, da hauhawar farashin kayan masarufi, ƙarin kudin lantarkin ya kara dagula musu lissafi.

A shafukan sada zumunta kamar su X wato Twitter da Facebook, 'yan Najeriya da dama sun bayyana taƙaicinsu da damuwarsu kan karin kudin wutar lantarkin.

Mun leƙa waɗannan shafukan domin zaƙulo wasu ra'ayoyin al'ummar Najeriya game da wannan ƙarin kudin lantarkin.

Wani mai amfani da shafin X, Shehu Gazali Sadiq ya rubuta a shafin nasa cewa

"Sun cire tallafin man fetur ba tare da kafa wani kwamiti ba. Sun kara kudin wutar lantarki ba tare da kafa kwamiti ba. Amma wajen ƙara mafi karancin albashi, sun kafa kwamitin da ba wanda ya san abin da suke yi. ’Yan siyasar Najeriya sun fi kowa zalunci a doron kasa."

Kauce wa Twitter, 1
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

Adamu Hayatu shi ma ya rubuta a shafinsa cewa

""Ajin A kaɗai" wannan babbar karya ce.

Naira 5,000 na ba da ma'awnin wutar 20.7kW ne kacal."

Kauce wa Twitter, 2
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 2

Kome kuma ya rubuta a shafinsa cewa

"Assalamu alaikum @aedcelectricity, ba mu sami wutar lantarki ba tun karfe 6:40 na yammacin jiya a Maitama, ɗaya daga cikin unguwar da ke Ajin A. Don Allah, gyara."

Kauce wa Twitter, 3
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 3

Onye Nkuzi, shi ma ya rubuta a shafinsa na X, inda ya ce

"Ai kuma babban layin wuta na ƙasa zai sake durƙushewa a cikin watanni biyu masu zuwa, duk da rubanya farashin wutar lantarki da duk azuzuwan A da B da C da dai sauransu." shirme ne."

Kauce wa Twitter, 4
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 4

Hamma kuma ya rubuta a shafinsa cewa;

"Lallai ya kamata ’yan Najeriya su bijire wa wannan karin kudin wutar lantarki da aka yi na rashin imani, naira 10,000 zai bayar da ma'aunin wutar 42 ne kawai, wanda kwana biyu ne kawai, don haka sai mutum ya sayi wutar lantarkin dubu 150 domin gudanar da rayuwar yau da kullum.

Ina kira ga ’yan Najeriya da ka da su amince da wannan muguwar dabi’a"

Kauce wa Twitter, 5
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 5

Abubakar Sidiq Usman shi ma ya rubuta a shafinsa cewa;

"To idan ba mu samu wutar lantarki ta sa’o’i 20 a kowace rana ba bayan biyan sama da Naira 225 kowane ma'aunin wutar lantarki ɗaya, mene ne hukuncin kamfanin samar da wutar lantarkin?:

Kauce wa Twitter, 6
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 6

Shi kuwa farfesa Jibrin Ibrahim a shafinsa na X ya ce;

"Suna ikirarin muna samun wutar lantarki na sama da sa'o'i 20 a rana don haka suka ninka adadin kudin lantarkin da muke biya amma kuma babu wani ɗan Najeriya da ke samun haka."

Kauce wa Twitter, 7
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 7

Rabe-raben masu samun lantarki

....

Asalin hoton, Getty Images

Sharfuddeen Zubair Mahmoud, tsohon janar manaja na hukumar samar da wutar lantarki na Najeriya kuma darektan hukumar ba da lantarki ta Kaduna ne kuma ya yi wa BBC bayanin jerin azuzuwan wutar lantarki.

Mahmoud ya ce shekarun baya da dama mutanen Najeriya kan yi kuka kan rashin samun wuta duk da cewa suna biyan kudin lantarki, da wannan koken ne ya ce hukamar samar da wuta ta fahimci cewa akwai ƙamshin gaskiya a koken nasu inda ya sa ta fitar da wannan sabon tsari.

A wannan tsarin ne Mahmoud ya ƙara da cewa hukumar ta zauna ta duba su waye ne ke samun wuta a rana, inda kuma aka gano cewa akwai waɗanda ke samun wutar har na tsawon awa 20 ko sama da haka ma.

Hakan ne ya sa hukumar ta ce dukkannin kamfanonin da ke samar da wutar lantarki su tabbatar cewa sun gyara ɓangarorin da ke samun wutar lantarkin a kullum.

"A ta haka ne aka ce duk waɗanda ke samun lantarki na awa 20 a rana, su ne suka faɗa a ajin A, kuma su aka ƙara wa kudin lantarki." in ji darektan.

" Akwai kuma ajin B wanda su kuma suna samun wuta ta tsawon sa'o'i 16 a kullum. Shi kuma ajin C kuma su ne ke samun wutar lantarki ta tsawon awa 12 a kullum."

Ya ƙara da cewa "Akwai ajin D kuma su suna samun wutar lantarki ta tsawon awa 8 a rana

"Ajin E kuwa suna samun wutar lantarki ta tsawon awa 4 a rana." in ji Mahmoud.

Ya ce farkon tsarin shi ne a cikin shekara biyu, ana sa burin tabbatar da cewa babu wanda a ƙasar nan da ke samun wutar lantarki ƙasa da awa 12.

Ta ya ya mutane za su gane ajin da suke?

Mahmoud ya ce yadda mutane za su gane ajin da suke shi ne duba shafukan intanet na dukkan kamfanonin da ke rarraba wutar lantarki a jihohi saboda duk za su buga, kuma tuni wasu suka buga sunayen dukannin unguwanni da wurare da azuzuwan da suke.

Ya kuma ce ita ma hukumar samar da wutar lantarki ta ƙasa ta buga a nata shafin na intanet ta kuma ce nan gaba kaɗan za ta saka a buga a jaridu da dama saboda mutane su fahimci ajin da suke.

Ga waɗanda ba su samu damar shiga shafin intanet ba, Mahmud ya ce za su iya tuntuɓar kwamitin da kamfanonin za su kafa inda za a tura bayanansu da lambobinsu ta saƙwannin wayar tarho.

"Na san ko wane kwastoma ya riga ya san ajin da yake tunda ba yanzu aka soma wannan abun na azuzuwa ba, kowane kwastoma ya san abin da yake biya."

Ya ce duk wanda bai ga sunan uguwarsa ba a ajin A da aka buga a shafin intanet, to, ƙarin farashin lantarkin bai shafe shi ba kuma ya ce akwai ƴan ajin A da suka koma ajin baya saboda ba a biya musu buƙata kamar yadda hukuma ta ce.

Shin ɗan wani ajin na iya samun kansa a ajin da ba nasa ba?

Daraktan ya ce ba zai yiwu wani da ke ajin E ya sami kansa yana biyan kudin lantarkin waɗanda ke ajin A ko na B ko na C ko na D ba.

Ya ƙara da cewa idan aka ce wata uguwa na cikin ajin A, duk kwastoman da ke wannan unguwar zai biya sabon farashin da aka fitar na lantarki.

Darektan ya kuma ce a tsarin da aka yi, ana son a cikin ko wanne wata shida akalla a dinga matsar da mutane gaba kamar a ce wanda suke ajin E na ƙarshe a matsar da su zuwa ajin D ko ajin C duk bayan wata shida, waɗanda suke ajin A kuma a matsar da su zuwa ajin B, ko kuma ƴan ajin B su koma zuwa ajin A ko ajin C duk bayan wata shida.

Ya ce idan kuma 'yan ajin A ba sa samun wuta yadda ya kamata kamar a ce suna samu ta tsawon awa 4 ko 8, yayin da ya kamata su sami na awa 20, ya ce toh gaskiya da akwai miskila saboda haka za a mayar da su ajin da ke samun wuta a adadin waɗannan awowi..

Darekta ya ce wannan ƙarin kawai ƴan ajin A aka yi wa.

"Daman kudin lantarkin aji-aji ne, ba kuɗin da ajin A ke biya ba ajin B za su biya ba."

"Ajin B na biyan ƙasa da abin da ajin A ke biya.Ajin C na biyan kudi ƙasa da abin da ajin B ke biya. Ajin D na biyan kudin lantarki ƙasa da abin da ajin C ke biya, hakazalika ma ajin E na biyan kuɗi ƙasa da abin da D ke biya." in ji Mahmoud.

Ya kuma ce kudin lantarkin da ajin B zuwa E suke biya ya danganta da kamfononin rarraba lantarki saboda kuɗin da suke sayar da lantarkin ya bambanta.

Ina jama'a za su kai ƙorafinsu?

Mahmoud ya ce, "a wannan sabon tsarin, kowane kamfanin da ke rarraba hasken lantarki, hukuma ta saka shi dole ya kafa wani kwamiti na ko-ta-kwana na ma'aikatansa kuma za su fadi sunayensu tare da buga sunayen a shafin intanet dinsu da lambobinsu da komai."

Darektan ya kara da cewa "sannan kuma za su aikawa duk wani kwastomominsu bayanan ta wayar tarho a matsayin saƙo cewa ga mutanen da suke mana aiki na ko-ta-kwana ko da suna da wani ƙorafi ko kuma wata tangarɗa da lantarkinsu ku yi musu magana."

"Sanna kuma kowace rana, kwamitin za su ringa buga yawan hasken lantarkin da suka bayar da awowin da suka bayar a dukannin waɗannan wuraren."

People are also reading