Home Back

Malawi: Jirgin Mataimakin Shugaban Ƙasa Ya Yi Hatsari, Mutanen Ciki Sun Mutu

legit.ng 2024/7/3
  • Rahotanni na nuni da cewa jirgin da ke dauke da mataimakin shugaban kasar Malawi, Saulos Klaus Chilima da mutane tara ya yi hatsari
  • Shugaban kasar Malawi, Lazarus Chakwera ne ya fitar da sanarwar yana mai cewa Saulos Chilima da mutanen sun mutu a hatsarin
  • A jiya Litinin ne muka ruwaito maku cewa jirgin sojojin Malawi, dauke da Chilima ya bace a sararin samaniya, kuma an gaza gano shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Malawi - Mataimakin shugaban kasar Malawi, Saulos Klaus Chilima da wasu mutane tara sun mutu a lokacin da jirgin sojin da suke tafiya a ciki ya yi hatsari.

Jirgin da ke dauke da Chilima, wanda ake ganin zai iya tsayawa takara a zaben shugaban kasa na badi, ya bace a ranar Litinin.

Chilima: Mataimakin kasar Malawi ya mutu
Jirgin da ke dauke da mataimakin shugaban Malawi ya yi hatsari, kowa ya mutu. Hoto: rbkomar Asali: Getty Images

Mataimakin shugaban kasar Malawi ya mutu

Shugaban kasar Malawi, Lazarus Chakwera ne ya fitar da sanarwar mutuwar mataimakin na shi a ranar Talata kamar yadda shafin Reuters ya ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina mai bakin cikin sanar da ku cewa mummunan abin da muke addu'ar kar ya faru, shi ne ya faru. Tawagar bincike da ceto sun gano jirgin a kusa da wani tsauni.
"Sun gano cewa babu wanda ya tsira daga wannan hatsarin sakamakon yadda jirgin ya tarwatse tare da komawa tarkace."

- In ji Shugaba Chakwera a wani jawabin kai tsaye ga al'ummar kasar Malawi.

"Wani abu ya faru da jirgin" - Chakwera

Jaridar BBC ta ruwaito Chakwera na cewa dukkanin fasinjojin da ke cikin jirgin sun mutu ne sakamakon hatsarin da ya faru kuma sojoji na hanyar dawo wa da gawarwakinsu.

Shugaban kasar ya ce:

"Duk da bin diddigi da kuma kwarewar ma'aikatan jirgin, wani mummunan abu ya faru da jirgin a lokacin da ya ke hanyar komawa Lilongwe, wanda ya sa ya yi hatsari."

Asali: Legit.ng

People are also reading