Home Back

Ɗan Shekara 13 Ya Kashe Kansa Bayan Jami’an Tsaro Sun Azabtar Da shi

leadership.ng 2024/6/26
Ɗan Shekara 13 Ya Kashe Kansa Bayan Jami’an Tsaro Sun Azabtar Da shi

Wani yaro mai shekaru 13 mai suna Wisdom Hashimu ya mutu ta hanyar rataye kansa a Unguwar Maigero da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wani soja da jami’an rundunar hadin gwiwa ta Cibilian Task Force a yankin sun azabtar da marigayin.

Marigayi Wisdom wadda ta aikata wannan aika-aika a harabar gidan da ke kan titin Lafiya Sarki an ce an zarge shi da laifin satar Naira 10,000 daga wata makwabciyarsu a ranar.

A wani rahoto da gidan Talabijin na Channels TB ta fitar, makwabciyarta mai shekaru 16 mai suna Hope, an ce ta gayyaci saurayinta mai suna Segun Samson, wanda soja ne a sansanin Bodi da ke Fatakwal, babban birnin jihar Ribers wanda ya shiga cikin maganar.

Sai dai an nemi kudi an rasa a lokacin ziyarar, wanda hakan ya sa Hope ta hada saurayin nata da Wisdom da kuma dan uwanta zuwa ofishin Cibilian JTF.

Wisdom wacce ke zana jarabawar Karamar Sakandare, an bayyana cewa wani soja da jami’an Cibilian JTF ne suka yi masa mugun duka.

Mahaifin Wisdom, Mista Saul, wanda ya zanta da manema labarai ya ce, “Maimakon su kai rahoto ga ‘yansanda, sai kawai sojan ya ja dan’uwan Wisdom da Hope, wadanda ake zargi da satar kudin zuwa ofishin cibilian JTF.

“A ofishin cibilian JTF, an yi wa Wisdom mugun duka har ya kasa tafiya. Ya koma gida inda aka fara kula da lafiyarsa.”

Sai dai kuma wani abin takaici da ya afku shi ne an tsinci gawar Wisdom ya rataye kansa a bayan gidansu.

Sai dai a yayin da yake magana cikin bacin rai, mahaifin ya ce ‘yan Cibilian JTF sun dauki doka a hannunsu ta hanyar azabtar da Wisdom.

“Amma, ni abin da tunanina ya bani, Cibilian JTF ne kawai suka lakada wa Wisdom duka har ta kai ga suma, yayin da kanin Hope ya tsira ya dawo gida.

“Bayan an yi mata tambayoyi a gida, kaninta Hope ya amsa laifin da ya aikata, bayan da aka gano Naira 9,000 a aljihunsa, ya ce ya riga ya kashe Naira 1,000,” a cewarsa.

Don haka dangin sun bukaci a yi adalci kan azabtarwa da ake zargin marigayi dansu wanda hakan ya kai ga kashe shi.

“Tun daga lokacin aka fara bincike. Kwamishinan ‘yansandan ya umarci sashen binciken manyan laifuka da ya dauki nauyin lamarin kuma duk wanda ke da hannu za a gurfanar da shi a gaban kotu domin tabbatar da adalci”

Wisdom da ke zana jarabawar karamar Sakandare, an bayyana cewa wani soja da jami’an Cibilian JTF ne suka yi masa mugun duka.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, Mansir Hassan, ya ce an fara bincike kan lamarin.

People are also reading