Sanusi II vs Aminu Ado: ’Yan Najeriya Sun Yi Martani Bayan Hukuncin Kotu a Kano
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - A yau Alhamis 20 ga watan Yunin 2024 Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan dambarwar sarautar Kano.
Kotun yayin hukuncin ta rushe matakin da Gwamna Abba Kabir ya dauka kan soke masarautn jihar guda biyar.
Sanusi II Vs Aminu: An fara zaman ɗari ɗari a Kano bayan hukuncin da kotu ta yanke
Hukuncin da kotun ta yi a Kano
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkalin kotun, Abdullahi Liman ya bayyana cewa duka matakan da Gwamna Abba Kabir ya dauka ba su da tasiri a yanzu.
'Yan Najeriya da dama sun yi martani mabanbanta kan wannan mataki na kotu inda kowa ke fadin albarkacin bakinsa.
Legit ta zakulo wasu daga cikin martanin jama'a daga sassan kasar baki daya kan hukuncin kotun:
@Northerner0:
"SLS zai sake rasa kujerarsa kenan a karo na biyu?."
@donpanacio:
"Na fada muku gwamnatin Kano da Majalisar jihar suna bata lokacinsu ne kawai, Alhaji Aminu Ado Bayero shi ne Sarkin Kano, ba za ka tashi kawai ka sauya sarki babu bincike ba, Sanusi kansa an bincike shi kafin cire shi, wannan shi ne doka."
@auwerl_serlies:
"Sanusi ne sarki har yanzu."
Sarkin Kano: Kotu ta soke nadin da aka yiwa Sanusi II? Ga karin haske kan hukuncin
@sukairaaj:
"HRH Sanus 1:1 Aminu, za mu je hutun karin lokaci."
@ChurcH94414:
"Ina fatan kuna sane da Ganduje ma ya saba umarnin kotu a shekarar 2015, abin dariya."
@ladoskyabays:
"Shin Babbar Kotun Tarayya tana da ta cewa a wannan lamari? a'a... alkalin kawai yana bata sunan bangaren shari'a ne."
Kun ji cewa Rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano ta roƙi jama'a su zauna lafiya a lokacin da ake dakon hukuncin Babbar Kotun Tarayya kan rigimar sarauta.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya fitar a Kano.
Asali: Legit.ng