Home Back

Diyar Ado Bayero Ta Turawa Shugaba Tinubu Sako, Tayi Zancen Rigimar Masarautar Kano

legit.ng 2024/7/6
  • Diyar marigayi Sarki Ado Bayero ta bukaci Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya duba halin da ‘yan Najeriya suke ciki da zummar kawo musu sauki
  • Zainab Ado Bayero, wanda ta ke fafutukar tabbatar da gwamnatin da al’umma za su mora ta ce akwai bukatar a gyara tunanin ‘yan kasar nan da suka tsani junansu
  • Da ta juya kan dambarwar masarautar Kano, diyar marigayin ta bayyana takaicin abin da ke faruwa a halin yanzu, inda ta bukaci kowane bangare ya yi taka tsan-tsan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Daya daga ‘ya’yan marigayi Ado Bayero, Zainab ta tunatar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu nauyin da ya rataya a wuyansa na kawo sauki ga halin da ‘yan Najeriya ke ciki.

Zainab Bayero, wacce ke rajin tabbatar da gwamnati domin al’umma ta bayyana cewa da yawa daga ‘yan kasar nan na cikin kuncin rayuwa.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Diyar marigayi sarkin Kano Ado Bayero ta tunawa Tinubu halin da 'yan kasa ke ciki Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Nigerian Tribune ta wallafa cewa diyar marigayi sarkin Kano Bayero na wanna batu ne a taron kan shirin tunawa da marigayi Ado Bayero shekaru 10 da rasuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce ya kamata shugaba Bola Tinubu ya dauki gabarar hade kan ‘yan Najeriya da a yanzu ke fama da kiyayyar juna a zukatansu.

Rikicin masarauta: ‘Ku nuna dattako,’ Bayero

Yayin da ake ci gaba da kallon kallo tsakanin sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, diyar marigayi sarki Ado Bayero ta ce kowa ya yi taka tsan-tsan.

New Telegraph ta tattaro cewa Zainab Ado Bayero, ta ce al’amarin babu dadi ko kodan, duk cewa ta amince da ana samun irin wannan a masarauta.

A gefe guda kuma ta bayyana takaicinta, inda ta ce bai kamata ‘yan siyasa su mayar da masarauta abin wasansu ba da haddasa rikici a masarautar.

Gwamnati za ta rage hauhawar farashi

A baya mun baku labarin cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana kokarin daukar matakan rage hauhawar farashin kayan abinci a kasar nan.

Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari ya bayyana cewa sun tanadi taki, ingantaccen iri da maganin kwari ga manoma domin habaka yabanya.

Asali: Legit.ng

People are also reading