Home Back

Koriya ta Kudu da Kasashen Afirka za su karfafa dangantaka

dw.com 2024/7/3
Shugaban Yoon Suk Yeol na Koriya ta Kudu
Shugaban Yoon Suk Yeol na Koriya ta Kudu

Ana sa ran kasashen Afirka 48 ciki har da shugabanni 25 za su halarci taron na kwanaki biyu, wanda zai mayar da hankali kan kasuwanci da kuma zuba jari. Shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol ya ce zai fadada taimakon kasar na raya kasashen Afirka kana ya kara karfafa hadin gwiwa kan ma'adanai da fasaha.

A halin yanzu dai, cinikayya a tsakanin bangarorin biyu ya gaza kashi biyu cikin 100 na kayayyakin da Koriyar ke shigar wa da kuma fitar wa daga kasarta, sai dai kuma gwamnatin Seoul da ta dogara a yanzu da China, na son inganta dangantaka da Afirka a fannonin albarkatun kasa da kuma ma'adanai da nufin fadada jajjircewarta a manyan masana'antun fasaha.

Shugaban ya kuma bukaci kasashen Afirka da su kara yin taka tsan-tsan da makwafciyarsa Koriya ta Arewa.

People are also reading