Home Back

Ana gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Iran

dw.com 2024/8/21
Hoto: AHMAD AL-RUBAYE/AFP

A Juma'ar nan ce al'ummar Iran ke komawa rumfunan zabe don kada kuri'a, a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, wanda ake fafata wa tsakanin mai ra'ayin rikau Saeed Jalili, da kuma Masoud Pezeshkian mai rajin kawo sauyi.

Karin bayani:Khamenei ya nemi fitowar masu zabe

A ranar 28 ga watan Yunin da ya gabata ne aka gudanar da zagayen farko na zaben, don maye gurbin tsohon shugaban kasar Ebrahim Raisi da ya mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu, a cikin watan Mayun da ya gabata, to sai dai babu 'dan takarar da ya samu rinjayen kuri'u sama da kashi 50 cikin 100 da za su ba shi damar lashe zaben kai tsaye.

An dai samu karancin masu yin zaben na zagayen farko, wanda ya samu kiraye-kirayen kaurace wa daga 'yan gwagwarmaya irin su Narges Mohammadi da ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel, da yanzu haka take daure a kurkuku.

People are also reading