Zaɓen Bayelsa: Kotu Ta Tanadi Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Gwamnan PDP
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamnan jihar Bayelsa ta tanadi hukunci a ƙarar da ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APC, Timipre Sylva, ya shigar.
Sylva, tsohon ƙaramin ministan man fetur ya kalubalanci nasarar Gwamna Doure Diri na jam'iyyar PDP a zaben da aka yi a watan Nuwamba, 2023.
Alƙalin kotun zaɓen mai shari'a Adekunle Adeleye ya sanar da cewa za a yanke hukuncin kowane lokaci daga zuwa kwanaki 180 kamar yadda doka ta tanada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bayyana cewa za a sanar da kowane ɓangare da zarar kotun ta zaɓi ranar da za ta karanto hukunci a shari'ar, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
A zaman da kotun ta yi ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu, 2024 kowane ɓangare ya miƙa rubutaccen bayanansa na ƙarshe ga alkali.
Yayin da jam'iyyar APC da ɗan takararta suka roƙi kotun ta amince da buƙatarsu saboda zaɓen cike yake da kura-kurai, PDP da Gwamna Diri sun nemi a kori ƙarar domin APC ba ta hujjoji.
Gwamna Diri ya hau kan karagar mulkin Bayelsa a 2020 a karon farko, sanna kuma ya samu nasarar lashe zaɓen gwamnan da aka yi a watan Nuwamban 2020 ya zarce zango na biyu.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa Diri na jam'iyyar PDP ya samu ƙuri'u 175,196 yayin da Sylva, ɗan takarar APC ya samu ƙuri'u 110,108.
Amma bayan hukumar zaɓe INEC ta sanar da sakamako, tsohon ministan ya kalubalanci ayyana Diri a matsayin wanda ya lashe zaɓen a gaban kotu.
A wani rahoton kuma masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC sun fara juyawa Ganduje baya kan batun dakatar da shi a gundumarsa da ke jihar Kano.
Wannan na zuwa ne bayan wani tsagin APC a gundumar Ganduje sun sake fitowa sun tabbatar da dakatar da shi a karo na biyu.
Asali: Legit.ng