Home Back

ZAFAFAN RADDIN ABBA GIDA-GIDA GA GANDUJE: Ba ka da kunya har ka ke borin-kunyar shekara takwas da ka yi ka na tafka gadangarƙama a Kano

premiumtimesng.com 2024/5/6
ZAFAFAN RADDIN ABBA GIDA-GIDA GA GANDUJE: Ba ka da kunya har ka ke borin-kunyar shekara takwas da ka yi ka na tafka gadangarƙama a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir-Yusuf, ya maida wa tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje zafafan raddi, dangane da zargin kasawar da ya ce gwamnatin Kano ta yanzu ta yi a watannin goma da ta yi ta na mulki.

Gwamna Abba ya ce shekaru takwas na mulkin Ganduje cike suke maƙil da gadangarƙamar almubazzaranci, handama, ragabza, almundahana, gidoga, gagarimar wawura da karkatar da maƙudan kuɗaɗen al’umma.

Ya ce Ganduje ya yi ƙaurin suna wajen sayar da kadarorin gwamnatin Jihar Kano, ya na maka kuɗaɗen aljifan sa. Wasu kadarorin kuma duk iyalan sa ya sayar wa su.

Cikin wata sanarwar manema labarai da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Abba, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar da yammacin Lahadi, Abba ya ce ya ji matuƙar takaicin yadda tsohon gwamna Ganduje saboda rashin kunya, har ya fito ya ke kantara ƙarairayi kan gwamnatin NNPP a Kano.

Gwamna Abba ya ce maimakon Ganduje ya fuskanci haƙƙi da alhakin wawuran kuɗaɗen da ya yi da kuma laifukan tarzomar lokutan zaɓe da ya haddasa a lokacin da ya na gwamna, sai ya ke borin kunya a yanzu, saboda bai san kunya ba.

Abba ya ce zango biyu na mulkin Ganduje cike fal suke da karkatar da kuɗaɗe da kuma ƙasa gudanar da ayyukan inganta al’umma da na raya jiha.

Ya ce Ganduje ya rura wutar ɓangaranci, zubar da jinainai wanda ya bar iyalan mutane da dama cikin rayuwar tarangahuma.

“Mu watanni takwas na farkon gwamnatin mu sun fi shekaru takwas na mulkin Ganduje, wanda banda lalata tasirin siyasa a Kano, ba abin da Ganduje ya yi,” inji Gwamna Yusuf.

A gefe ɗaya kuma gwamnan ya shawarci Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, da tsohon Gwamna Ganduje su yi haramar gaganiya da raƙamniyar kare kan su a kotu, maimakon ƙara tona asirin kan su da suke yi a kafafen yaɗa labarai.

People are also reading