Home Back

Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya Doguwa naira miliyan 25 kan zargin kisa da ta yi masa

premiumtimesng.com 2024/7/6
Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya Doguwa naira miliyan 25 kan zargin kisa da ta yi masa

Kotu a Abuja ta umarci gwamnatin Kano ta biya naira miliyan 25 ga dan majalisa Ado doguwa, bisa abinda ta kira kazafi da ta yi masa na aikata kisan kai.

An zarge shi da kisan wasu mutane uku da ake kyautata zaton ‘yan jam’iyyar adawa ta New Nigerian People’s Party (NNPP) ne a lokacin yayin babban zaben 25 ga Fabrairun 2023.

Alkali D.U. Okorowo ya wanke Doguwa daga zargin kisan kai a lokacin da ya ke yanke hukuncin.

Kotun dai ta haramtawa gwamnatin jihar kamawa da tsare shi da kuma gurfanar da shi gaban kotu, inda ta ce laifuffukan da aka kirkira a sashe na 126 da 128 na dokar zabe ta 2022 na tarayya ne, ‘yan sanda sun bincike yadda ya kamata, kuma an wanke Doguwa tas-tas sumul lumui.

A hukuncin da ya yanke, Okoro ya ce za a biya Doguwa wannan kudi ne saboda jefa shi cikin wani yanayi na damuwa a dalilin wannan sharri da kazafi da gwamnatin Kano.

People are also reading