Home Back

Ziyarar Xi Jinping A Turai Ta Fitar Da Muryar Kiyaye Zaman Lafiya Da Yin Hadin Gwiwa

leadership.ng 2024/6/26
Ziyarar Xi Jinping A Turai Ta Fitar Da Muryar Kiyaye Zaman Lafiya Da Yin Hadin Gwiwa

Tsakanin ranakun 5 zuwa 10 ga watan nan da muke ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gudanar da ziyarar aiki a kasashen Turai guda uku, wadanda suka hada da Faransa, da Serbia, da kuma Hungary. Ziyararsa a kasashen uku ta samar da muhimmin tasiri ga kasar Sin da kasashen Turai, har ma da dukkani kasashen duniya, ta kuma samar da dabaru ga kasa da kasa a wannan halin sauye-sauye da duniya ke fuskanta.

Nisan dake tsakanin kasar Sin da kasashen Faransa da Serbia da kuma Hungary ba zai iya hana su zurfafa zumuncin dake tsakaninsu ba. A yayin ziyarar shugaba Xi a wadannan kasashe, kasar Sin da kasashen uku sun kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama, lamarin da ya nuna cewa, komai nisan dake tsakanin kasa da kasa, za mu iya taimakawa juna, da cimma moriyar juna, idan aka girmama juna kuma aka hada kai.

A yayin da yake ziyarar aiki a kasashen Turai, Xi Jinping ya yi cikakken bayani kan tasirin da kasar Sin za ta yi kan kasa da kasa ta hanyar neman zamanintar da kanta, da kuma gudummawar da kasar za ta baiwa kasa da kasa a lokacin da take neman bunkasuwar tattalin arzikinta. Xi Jinping ya jaddada cewa, yadda kasar Sin ke kokarin inganta bunkasuwarta mai inganci, da gaggauta aikin raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, zai samar da karin kasuwanni ga kasashen Turai da ma sauran kasashen duniya, tare da samar da karin damammaki ga kasashen duniya wajen habaka hadin gwiwarsu domin cimma moriyar juna.

Xi Jinping ya bayyana cewa, halin da kasar Sin take ciki, da zaman rayuwar al’ummomin kasar Sin sun sauya matuka, amma abin da bai sauya ba shi ne, halayen al’ummomin kasar Sin na son zaman lafiya da taimakawa juna, Sinawa mutane ne masu fahimtar juna da neman adalci. Ya ce, ba kawai muna son samun farfadowar kasar Sin ba, haka kuma, muna son tallafawa al’ummomin kasashen duniya don su ji dadin rayuwarsu, su kuma raya kansu. Kasar Sin tana dukufa wajen yin hadin gwiwa da kasashen duniya wajen neman ci gaba tare, wannan shi ne ainihin burin kasar Sin na gina al’ummar dukkanin bil Adama mai makoma ta bai daya. Kana, kasar Sin mai karfi ba za ta zama barazana ga sauran kasashen duniya ba.

Haka kuma, dangane da ziyarar aikin a kasashen uku, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasa Wang Yi ya gabatar da karin bayani. Inda ya ce kasar Faransa, ita ce kasa ta farko da ta kulla huldar diflomasiyya da Jamhuriyyar Jama’ar Kasar Sin cikin manyan kasashen yammacin duniya, kuma tana bin ka’idar ’yancin kai, da mulkin kai a ko da yaushe.

Wang Yi ya kara da cewa, ziyarar aiki da shugaba Xi Jinping ya yi a kasar Faransa, ta kasance muhimmin mataki a jadawalin taya murnar cika shekaru 60 da kulluwar huldar diflomasiyya a tsakanin Sin da Faransa. A yayin ziyararsa a kasar, bangarorin biyu sun fidda sanarwar hadin gwiwa guda 4, wadanda suka hada da sanarwar hadin gwiwa kan yanayin Gabas ta Tsakiya, da sanarwar hadin gwiwa kan kare nau’o’in halittu da tekuna, da sanarwar hadin gwiwa kan ayyukan gona, da kuma sanarwar hadin gwiwa kan fasahar AI, da harkokin kasashen duniya. Ban da haka kuma, sun kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa kimanin 20.

Haka kuma, Wang Yi ya ce, kasar Serbia ita ce abokiyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare ta farko ga kasar Sin a yankin Turai. Kuma a ’yan shekarun nan, shugaba Xi Jinping da shugaba Aleksandar Vucic sun kulla dangantakar fahimtar juna mai zurfi a tsakaninsu, bisa mu’amalar da suka yi, inda suka cimma nasarar raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin sauri, kuma kamar yadda ake fata. A wannan karo, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sake yin ziyarar aiki a kasar Serbia bisa gayyatar da shugaba Vucic ya yi masa, inda shugabannin biyu suka cimma matsaya daya a fannin gina al’ummar Sin da Serbia mai makoma ta bai daya.

A yayin da yake hira da manema labarai tare da shugaban kasar Serbia Aleksandar Vucic, Xi Jinping ya kuma sanar da wasu matakai 6 da za su tallafawa gina al’ummar Sin da Serbia mai makoma ta bai daya.

Na farko, bisa hadin gwiwar Sin da Serbia, yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci tsakanin kasashen biyu za ta fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli.

Na biyu, kasar Sin tana goyon bayan Serbia ta karbi bakuncin bikin baje koli na duniya na shekarar 2027, kuma za ta tura tawagar da za ta halarci bikin.

Na uku, a shirye kasar Sin take ta karbi kayayyaki masu inganci da ma amfanin gona daga Serbia.

Na hudu, cikin shekaru 3 masu zuwa, bangaren Sin zai taimakawa matasa 50 masana kimiyya daga Serbia a shirye-shiryen musaya na kasar.

Na biyar, har ila yau cikin shekaru 3 masu zuwa, za a gayyaci jimilar matasan Serbia 300 domin su yi karatu a kasar Sin.

Na shida, kasar Sin na maraba da Serbia ta kara yawan zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakanin Belgrade da Shanghai, tare da karfafawa kamfanonin jiragen saman kasashen biyu gwiwar kaddamar da zirga-zirga kai tsaye tsakanin biranen Belgrade da Guangzhou.

Sa’an nan kuma, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Hungary tana cikin kasashen dake kan gaba, da suka yi saurin kulla huldar diflomasiyya da jamhuriyar jama’ar Sin. A bana, ake cika shekaru 75 da kulla huldar diflomasiyyar a tsakanin kasashen biyu. Cikin wadannan shekarun da suka gabata, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta bunkasa yadda ya kamata, inda suka cimma nasarar karfafa fahimtar juna a fannin siyasa, yayin da kuma suka samu sakamako da dama, bisa hadin gwiwar dake tsakaninsu. Yanzu haka, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana cikin yanayi mai kyau, ta kuma kasance abar koyi a fannin raya sabon salon dangantaka tsakanin kasa da kasa.

Wang Yi ya kuma kara da cewa, a shekarar 2025 mai zuwa, za a cika shekaru 50 da kulla dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kungiyar tarayyar kasashen Turai wato EU, kuma yanzu ana cikin muhimmin lokaci na ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin Sin da EU.

Ya ce, a birnin Paris na kasar Faransa, a lokaci guda shugaba Xi ya gana da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, da shugabar hukumar gudanarwar kungiyar EU Ursula von der Leyen tare. A yayin ganawarsu, Xi ya yi bayani mai zurfi kan dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, ya kuma bayyana cewa, a matsayin manyan karfi cikin kasashen duniya, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kungiyar EU tana yin muhimmin tasiri ga zaman lafiya, da zaman karko, da kuma wadatar kasashen duniya.

A lokacin ziyararsa, shugaba Xi Jinping ya yi musayar ra’ayoyi da shugabannin kungiyar EU, game da batutuwan dake shafar rikicin Ukraine, da rikicin dake tsakanin Isra’ila da Falesdinu, da ma sauran harkokin kasa da kasa dake jan hankulan jama’ar kasashen duniya. Xi Jinping ya ce, kamata ya yi kasar Sin da kasashen Turai su hada kansu, wajen hana bazuwa, da ci gaban rikice-rikicen, tare da samar da damammakin yin shawarwari a tsakanin bangarorin da abun ya shafa, domin kare tsaron makamashi, da wadatar hatsi ga kasashen duniya, da kuma tabbatar da yanayin zaman karko a fannin samar da kayayyaki a tsakanin kasashen duniya.

Da yake tsokaci kan rikicin Isra’ila da Falesdinu kuwa, shugaba Xi ya jaddada cewa, abu mafi muhimmanci a halin yanzu, shi ne tsagaita bude wuta cikin sauri bisa dukkanin fannoni, da samar da taimakon jin kai yadda ya kamata, kana, a aiwatar da “daftarin kafa kasashe biyu”, a matsayin hanyar da ta dace ta warware matsalar daga tushe. Kasar Sin tana goyon bayan a kira taron shimfida zaman lafiya na kasa da kasa cikin sauri, domin inganta aikin warware matsalar Falesdinu cikin yanayi na adalci, kuma daga dukkan fannoni.

Wang Yi ya ce, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen kare gaskiyar tarihi, da yanayin adalci da zaman lafiya, lamarin da ya sa ta samu amincewa, da yabo daga gamayyar kasa da kasa, yayin da take ba da muhimmiyar gudummawa a fannin kare zaman lafiya, da zaman karko tsakanin kasashen duniya.

Haka zalika kuma, ziyarar aiki da mai dakin shugaban kasar Sin Xi Jinping, Peng Liyuan ta yi a kasashen ta kuma ja hankulan al’umma sosai. A wannan karo, ta halarci bukukuwa da taruka sama da guda 20 tare da Xi Jinping, ta kuma yi shawarwari masu ma’ana tare da matan shugabannin kasashen uku. A yayin ziyarce-ziyarcenta, Peng Liyuan ta zanta da ’yan mata da dalibai na kasashen uku, inda ta yi fatan za su koyi Sinanci da kara fahimtarsu game da harkokin Sin. Lamarin da ya karawa al’ummomin kasashen sha’awarsu kan harkokin kasar Sin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang).

People are also reading