Kotu ta Tasa Keyar 'Sanata' Zuwa Kurkuku Saboda Zargin Damfarar 'Yar Kasar Waje
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Wata babbar da ke zamanta a Gwagwalada, Abuja ta yiwa sanatan bogi, Tom Makwe daurin shekara biyu bayan kama shi da laifi damfara.
Mista Makwe ya damfari wata 'yar kasar Sufaniya, Maria Del Rosario San Jose Garces tsabar kudi €47,000 ta kafar intanet.
Vanguard News ta wallafa cewa hukumar EFCC ce ta gurfanar da Makwe gaban kotu kan tuhume-tuhume guda biyu na damfara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar EFCC ta bayyanawa kotu cewa Tom Makwe ya damfari 'yar kasar Sufaniya ta hanyar asusun bitcoin da ya bude.
Lauyar EFCC, Deborah Adamu-Eteh ta shaidawa kotu cewa wanda ake zargi ya yi basaja ne a zuwan shi ne Sanata Tompolo da wani Bryan tsakanin 12 Nuwamba, 2021 zuwa 12 Disamba, 2021.
Jaridar Guardian ta wallafa cewa ana zarginsa da sake aikata damfarar a shekarar 2023, lamarin da ya amsa cewa ya yi, sannan ya nemi kotu ta sassauta masa.
A wani labarin kun ji cewa kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta yanke hukunci kan wadansu makudan kudi da ake zargin tsohon gwamnan CBN da boyewa.
Kotun ta umarci Godwin Emefiele ya mayar da makudan kudin da yawansu ya kai Dala Miliyan 1.4 ga asusun gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng