Home Back

Netherlands za ta kara da Austria ko Turkiya a kwata fainal a Euro 2024

bbc.com 2024/10/5
Netherlands

Asalin hoton, Getty Images

Tawagar ƙwallon kafa ta Netherlands ta kai daf da na kusa da na karshe, bayan da ta ci Romania 3-0 a zagaye na biyu a Euro 2024 ranar Talata.

Netherlands ta fara cin ƙwallo a minti na 20 da take leda ta hannun Cody Gakpo, kuma haka suka je hutu.

Saura minti bakwai a tashi daga karawar da aka yi a Allianz Arena, Netherlands ta kara na biyu ta hannun Donyell Malen, wanda ya kara na uku a raga.

Kenan Neterlands za ta buga kwata fainal ranar Asabar da duk wadda ta yi nasara a karawa tsakanin Austria da Turkiya ranar Talata.

Romania ta kawo wannan gurbin, bayan da ta yi ta daya a rukuni na biyar da maki hudu.

Ita kuwa Netherlands ta uku ta yi a rukuni na hudu da maki hudu

Wannan shi ne karo na 14 da suka fafata a tsakaninsu a dukkan karawa, inda Netherlands ta yi nasara 10, Romania ta ci wasa daya tal da canjaras uku.

Ƴan wasan Romania 11: Nita, Ratiu, Dragusin, Burca, Mogos, Marius Marin, Man, Razvan Marin, Stanciu, Hagi, Dragus.

Masu zaman benci: Rus, Nedelcearu, Alibec, Cicaldau, Puscas, Moldovan, Mihaila, Olaru, Tarnovanu, Sorescu, Racovitan, Birligea, Sut.

Ƴan wasan Netherlands 11: Verbruggen, Dumfries, de Vrij, van Dijk, Ake, Schouten, Reijnders, Bergwijn, Simons, Gakpo, Depay.

Masu zaman beenci: Geertruida, de Ligt, Wijnaldum, Weghorst, Frimpong, Bijlow, van de Ven, Veerman, Blind, Brobbey, Maatsen, Zirkzee, Flekken, Gravenberch, Malen.

Wasannin quarter final a Euro 2024

Ranar Juma'a 5 ga watan Yuli

  • Sifaniya da Jamus a Stuttgart.
  • Portugal da Faransa a Hamburg.

Ranar Asabar 6 ga watan Yuli

  • Ingila da Switzerland a Dusseldorf.
  • Netherlands da Austria/Turkey a Berlin.
People are also reading