Home Back

Hukuma Ta Koka Da Yadda Masu Mulki Ke Tauye Hakkin Al’umma

leadership.ng 2024/7/2

Hukumar kare hakkin Bil’adama ta kasa (NHRC) ta ce ta amshi koke san cin zaraf-in take hakkin Bil’adama har guda 55,218 a watan Mayu da tattaro a jihohin da suke fadin Nijeriya, manyan korafe-korafe an samesu ne a kan masu madafun iko da suke jihohi daban-daban.

Sakataren hukumar, Dakta Anthony Ojukwu shi ne ya shaida hakan a makon jiya, yayin da ke gabatar da bayani kan yawan kesa-kesan cin zarafin mutane da aka samu a watan Mayu da ya gudana a Abuja. Ya nuna takaicinsa kan cewa kaso mafi tsoka na kauye hakkin an samesu ne kan masu madafin iko.

Ya kuma nuna damuwa kan cewa masu rike da madafun iko da ya dace a ce suke tabbatar da yin duk mai yiyuwa domin ganin an kare hakkin al’umma, ba wai su kasance ja gaba wajen tauye musu hakkinsu ba.

Ojukwu ya nuna cewa akwai bukatar gwamnatocin jihohi da na tarayya da su dauki kwararan matakan shawo kan cin zarafin mutane ta hanyar aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta samar da ilimi ga kowa, kiwon lafiya, gidaje, da kuma samar da damarmakin ayyukan yi.

Ya ce hakan zai taimaka wajen kare hakkin jama’a da kuma ba su damar morar tattalin arzikinsu, jin dadi da walwa hadi da hakkin al’adu ba tare da nuna bam-bance-bambance ko tsangwama ba.

Da yake nuna takaici kan yadda kashe-kashe da garkuwa da mutane ke ci gaba da karuwa, babban Lauyan Nijeriya (SAN) ya yi tambayar kan yadda ake samun karuwar kamewa da tsare ‘yan jarida a kasar nan, kari kan yawan kashe jami’an tsaro, karuwar cin zarafin yara kanana gami da tasirin sauye-sauyen tattalin arziki wanda a cewarsa hakan na kara rage wa jama’a jin dadin hakkinsu a fadin kasar nan.

Shugaban NHRC ya kuma nuna takaicin hukumar na cewa a watan Mayu, sun shaidi korafe-korafen keta wa yara kanana haddi tare da cewa sama da kesa-kesai 31,288 da 7,560 an shigar da su ne kan masu madafun iko da wadanda ba su rike da madafun iko a cikin wannan wa’adin.

Ya ce, wannan adadin na tauye hakkin jama’a na zuwa ne dukd a kokarin da hukumar ke yi na dakile hakan. Ya ce, dole ne a nanata muhimmanci da ke akwai wajen bin matakan da suka dace domin wanzar da gaskiya, da kuma tabbatar da cewa jami’an tsaro na bin matakan da suka dace daidai da yadda doka ya tanadar musu.

A cewarsa, hukumar ta kuma samu rahoton kashe-kashe 298 da garkuwa da mu-tane 360 a cikin watan na Mayu da ‘yan bindiga dadi suka aikata.

Ya bukaci gwamnati da ta tashi tsaye wajen magance matsalar tauye hakkin jama’a da kuma tabbatar da cewa jama’a na cin gajiyar tattalin arzikinsu, walwala da jin dadi da kuma al’adu ba tare da nuna bambanci ko tsangwama ba.

People are also reading