Home Back

‘Yan sanda sun kama matar da ta yi karyar garkuwa da ita sannan ta yi wa kanta farashin kudin fansa N4.8m

premiumtimesng.com 2024/5/13
Ƴan sanda sun damke wasu abokai ƴan kungiyar matsafa dake tsafi da kawunan mutane a Ilori

Rundunar ‘yan sanda a jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya, ta kama wasu mutane uku da ake zargi masu garkuwa da mutane ne, ciki har da wata mata da ta yi karyar sace ta sanna ta yi wa kanta kudin fansa har Naira miliyan 4.8.

A cikin wata sanarwa da aka buga a ranar Litinin, mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, Chidi Nwabuzor, ya ce an kama su ne ta dabara amfani da fasahar zamani.

Nwabuzor, Sufeton ‘yan sanda, ya bayyana matar da Blessing Ogunu, ma’aikaciyar Bliss Legacy Limited da ke garin Benin.

Sauran wadanda ake zargin su ne Esther Anthony da Ukpebor Joel.

“Lokacin da ake yi mata tambayoyi, Blessing Ogunu ta amsa cewa ta shirya duk yadda aka yi garkuwa da ita ne saboda kamfaninta ya ki bai wa wani mutum fili da suka karbi kudi a wurinsa.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce wanda ake zargin, ya amsa laifin hada baki da saurayin ta da wasu mutane uku wajen yin garkuwa da ita, domin samun kudi a hannun ‘yar uwarta dake zaune a kasashen waje.

People are also reading