Home Back

Jam'iyyar RHDP mai mulki na son Ouattara ya sake tazarce

dw.com 2024/7/3
Hoto: Ange Servais Mahouena/Office President Ivory Coast

Kakakin kawancen kawancen jam'iyyun da ke mulkin na kasar Gilbert Koné Kafana ne ya bayana haka, a wani mataki na yi wa Shugaba Ouattara tayin tazarce, duk da yake shugaban bai fito karara ya bayyana manufarsa ba.

Gilbert Kafana ya ce Alassane Ouattara ne dan takarar jam'iyyar da ke mulki, kana za mu bukace shi ya amince da wannan kuduri idan lokaci ya yi.

Mai shekaru 82 a duniya Shugaba Ouattara na kan karagar mulki ne tun a shekarar 2011, bayan wa'adi na biyu shugaban ya sake kundin tsarin mulki a wani mataki na ci gaba da kasancewa kan madafan iko.

People are also reading