Home Back

Gwamnoni ba za su iya biyan abinda ya haura N70,000 a albashi ba

legit.ng 2024/10/4
  • Gwamnonin jihohin Najeriya sun yi taro kan mafi ƙarancin albashi yayin da kwamitin da aka kafa ke ci gaba da tattaunawa da ƴan kwadago
  • Wata majiya ta bayyana cewa gwamnoni ba za su iya biya abin da ya haura N70,000 ba bisa la'akari da yanayin tattalin arziki
  • A kwanakin baya Gwamna AbdulRazak na jihar Kwara ya sanar da cewa jihohi za su biya ƙarin albashi daidai da aljihunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Gwamnonin jihohi a Najeriya sun bayyana adadin da za su iya biya a matsayin mafi ƙarancin albashi a loƙacin da ake ci gaba da tattaunawa.

A wani taro da suka yi a Abuja jiya Alhamis, shugabannik jihohin sun yi duba trae da nazari kan yanayin tattalin arziƙi sannan suka karƙare ba za suniƴa biyan abin da ya haura N70,000 ba.

Taron gwamnonin jihohi.
Gwamnoni ba za su iya biyan abinda ya haura N70,000 a albashi ba Hoto: Abdulrahman AbdulRazaq Asali: Twitter

Kamar yadda The Nation ta tattaro, gwamnonin sun yi fatali da tayin N100,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi kamar yadda wasu ke yaɗawa.

Wasu majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa gwamnonin sun yi zama a Abuja karƙashin ƙungiyarsu NGF domin duba buƙatar ƴan kwadago.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun yi nazari kan tayin N60,000 da gwamnatin tarayya ta gabatar a baya da kuma N70,000 wanda gwamnatin jihar Edo ta fara biya a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Wata majiya a taron ta ce:

"Bayan dogon nazari kan mafi karancin albashi, mun yanke shawarar duba tsakanin N60,000 zuwa N70,000 a wata. Ba mu iya cimma matsaya ɗaya ba."

Bayan sun gaza cimma matsaya guda kan ƙarin albashin, NGF ta kafa kwamiti karƙashin jagorancin Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.

Uzodimma shi ne shugaban kungiyar gwamnonin da aka zaɓa karƙashin inuwar All rogressive Congress watau APC mai mulkin ƙasa.

Matsayin gwamnonin na jiya ya yi daidai da kalaman da shugaban NGF kuma gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya yi a baya.

Idan baku manta ba Gwamna  AbdulRazaq ya ce jihohin za su amince kuma su fara biyan mafi karancin albashi idan bai wuce ƙima ba.

Edun ya miƙa lissafin albashi ga Tinubu

Rahoto ya zo cewa Ministan kudi, Wale Edun ya miƙawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu rahoton sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ministan wa'adin sa'o'i 48 ya tattara bayanai ya miƙa masa.

Asali: Legit.ng

People are also reading