Home Back

An Cafke Motocin Dako 50 Makare Da Abinci Za Su Shiga Nijar A Zamfara

leadership.ng 2024/4/27
An Cafke Motocin Dako 50 Makare Da Abinci Za Su Shiga Nijar A Zamfara

Hukumar Sufuri ta Jihar Zamfara ta kama manyan motoci 50 da ke jigilar kayan abinci daga kasar nan za su shiga Jamhuriyar Nijar.

Hukumar, wacce ke aiwatar da umarnin shugaban kasa da ke da nufin kawo karshen matsalar karancin abinci da tara kaya, ta hana motocin da ke cike da hatsi iri-iri fita daga kasar.

Idan ba a manta ba a ranar Alhamis din da ta gabata Shugaban Kasa Bola Tinubu ya umurci manyan jami’ai uku da suka hada da Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro Nuhu Ribadu, da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Kayode Egbetokun da kuma Babban Daraktan Ma’aikatar Harkokin Gwamnati Yusuf Bichi da su hada kai da gwamnonin jahohi domin ganin an dakile mummunar dabi’ar nan boye kayan abinci.

An dauki matakin ne a yayin ganawar da shugaban kasar ya yi da gwamnonin a Abuja kan matsalar karancin abinci da ake fama da ita a halin yanzu sakamakon hauhawar farashin man fetur bayan cire tallafi da kuma rashin isasshiyar noma saboda ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane.

A ranar Lahadin da ta gabata ne Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta ce ta dakatar da tireloli 15 da ke jigilar kayan abinci ta kan iyakokin Sokoto zuwa Jamhuriyar Nijar.

Kazalika, gwamnatin Jihar Kano ta rufe rumfunan ajiya guda 10 da aka ce suna tara kayan abinci.

Da yake tabbatar da kama manyan motocin guda 50 a Zamfara, Shehu Sani, dan asalin garin Zurmi da ke Karamar Hukumar Zurmi a jihar, ya shaida wa wani wakilinmu ta wayar tarho a ranar Litinin da ta gabata cewa, an tare motocin ne a Kauyen Gidan Jaja, kusa da garin. Wanda ke kan iyakar Nieriya da Jamhuriyar Nijar.

Kakakin ZARTO, Sale Shinkafi, ya yi zargin cewa manyan motocin na yunkurin safarar kayayyakin abinci ne zuwa Jamhuriyar Nijar.

Ya ce, “Mutanenmu sun tare motoci 50 makil da hatsi iri-iri a lokacin da suke kokarin fitar da su daga kasar. Mun umurci masu su koma su sayar wa ‘yan Nijeriya kayayyakin a kan farashin da ya dace.”

Shinkafi ya bayyana cewa motocin ba su da rakiyar jami’an hukumar amma an umurce su ne kawai su koma yankunansu su sayar da kayayyakin a farashi mai sauki.

Ya ce, “Kun san cewa babban abin da ke damunmu shi ne mu tabbatar da cewa ba a fitar da kayan abinci daga kasar nan ta barauniyar hanya ba. Mun ki ba su damar shiga Jamhuriyar Nijar ne kawai.”

 
People are also reading