Home Back

Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Murna Ga Makon Yin Cudanya Tsakanin Matasan Sin Da Amurka

leadership.ng 4 days ago
Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Murna Ga Makon Yin Cudanya Tsakanin Matasan Sin Da Amurka 

Yau litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga bikin makon yin cudanya tsakanin matasan Sin da Amurka mai taken “Bond with Kuliang”.

A cikin sakon, Xi Jinping ya bayyana cewa, yadda aka kulla zumunta tsakanin al’ummar Sin da Amurka a Kuliang, wanda ya kwashe tsawon karni daya, wani kyakkyawan labari ne na mu’amalar sada zumunci tsakanin al’ummar kasashen biyu. Kuma yana farin cikin ganin matasan da suka fito daga bangarori daban daban na Sin da Amurka sun hadu a birnin Fuzhou, don waiwayen kyawawan abubuwan da suka faru a Kuling, da gadon kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da nufin karfafa cudanya da fahimtar juna a tsakanin jama’ar kasashen biyu.

Baya ga haka, Xi Jinping ya jaddada cewa, matasa su ne suka fi kowa kuzari da buri, kuma makomar dangantakar Sin da Amurka ta ta’allaka ne ga matasa. A cewar shugaba Xi, yana fatan matasan za su yi mu’amala mai zurfi, da inganta zumunci, da fahimtar juna, da tafiya kafada da kafada, da sada zumunci tsakanin Sin da Amurka, da taka rawa wajen ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba yadda ya kamata, kana da aiki tare da al’ummun kasa da kasa don tabbatar da zaman lafiya, da inganta samun ci gaba da kuma wadata tare. (Bilkisu Xin)

People are also reading