Home Back

Tsohuwar Minista Ta Fusata, Ta Ce Ba Za Ta Komawa Sabon Taken Najeriya ba

legit.ng 2024/7/1
  • Tsohuwar ministar ilimi, Obiageli Ezekwesili ta fusata kan yadda aka dawo da tsohon taken Najeriya maimakon 'Arise O Compatriots'
  • Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan dokar dawo da tsohon taken kasar da turawa suka hada mata ta 'Nigeria we hail thee'
  • Obiageli Ezekwesili ta sha alwashin ba za ta taba rera sabon taken ba domin a ganinta dawo da shi ba shi da amfani ga 'yan Najeriya A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Tsohuwar ministar ilimi a Najeriya Obiageli Ezekwesili ta ce babu abin da zai sa ta koma rera tsohon taken Najeriya da aka dawo da shi. A yau ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar dawo da 'Nigeria we hail thee' ya maye gurbin 'Arise O Compatriots' a matsayin taken Najeriya.
Oby Ezekwesili
Tsohuwar minista ta yi watsi da sabon taken Najeriya Hoto: Oby Ezekwesili Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa tsohuwar ministar sam dokar ba ta da wani amfani ga 'yan Najeriya, kuma duk mai kishin kasa ya san haka.

'Ba zan taba rera ta ba,' Ezekwesili

Tsohuwar ministar ilimin kasar nan, Obiageli Ezekwesili ta ce ba za ta taba rera sabon taken Najeriya ba.

Ta bayyana haka ne cikin fushi bayan shugaban kasa ya amince da kudurin dawo da taken, kamar yadda Nairaland ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga yanzu dai 'yan Najeriya za su rika rera tsohon taken da aka dawo da shi inda bukatar hakan ta taso.

Ta ce idan a bukaci ta rera taken Najeriya za ta rera 'Arise, O compatriots' da wasu suka saba rerewa kuma aka koya musu a makaranta.

Muhimman abubuwan taken Najeriya

A baya mun kawo muku cewa akwai muhimman abubuwa shida a tattare da sabon taken Najeriya na 'Nigeria we hail thee'.

A yau ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar da ta maye gurbin 'Arise O Compatriots' da sabon taken.

Asali: Legit.ng

People are also reading