Home Back

Bola Tinubu Ya Ɗauki Mataki Kan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi a Taron Majalisar Zartarwa

legit.ng 5 days ago
  • Majalisar zartarwa FEC karkashin Bola Ahmed Tinubu ta jingine rahoton kwamitin sabon mafi ƙarancin albashi a taron yau Talata
  • Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ya ce majalisar ta yi haka ne domin bai wa Tinubu lokaci ya ƙara nazari da neman shawarwari
  • Ya ce kwamitin da aka kafa kan sabon albashin ya miƙa rahotonsa amma ba zai yiwu FEC ta ɗauki mataki ba duba da lamarin ya shafi ɓangarori da dama

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) ta jingine kundin da aka gabatar kan sabon mafi karancin albashi a taron yau Talata a Aso Villa.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma na ƙasa, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar a fadar gwamnatin Najeriya.

Shugaban Kasa, Bola Tinubu.
Majalisar zartarwa ta kasa FEC ta jingine batun sabon mafi karancin albashi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Mohammed Idrisya shaidawa masu ɗauko rahoton gidan gwamnati cewa ajendojoji 39 aka gabatar a taron yau kuma majalisar ta duba su duka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangane da batun mafi ƙarancin albashi, ministan ya tabbatar da cewa kwamitin da aka kafa ya miƙa rahoton aikin da ya yi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kwamitin mafi karancin albashin da aka kafa ya ƙunshi wakilan kananan hukumomi, jihohi, kungiyoyin kwadago NLC da TUC da kuma gwamnatin tarayya.

Sai dai ministan ya ce majalisar ba za ta iya yanke hukunci a kan batun ba saboda ya shafi kananan hukumomi, jihohi, kamfanoni masu zaman kansu da ƴan kwadago.

Mohammed ya ƙara da cewa an jingine rahoto kan sabon mafi ƙarancin albashi ne domin bai wa shugaban ƙasa damar tuntuɓa da neman ƙarin shawarwari.

A cewarsa, Tinubu zai sake nazari kuma ya nemi shawarwari kafin ya miƙa kudirin sabon albashin ga majalisar tarayya, Channels tv ta ruwaito.

NLC ta nemi Tinubu ya ɗauki N250,000

A wani rahoton na daban kuma ƙungiyar kwadago ta yi kira ga Bola Ahmed Tinubu ya nuna ƙaunar da yake yiwa ma'aikata ta hanyar amincewa da N250,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

NLC ta bayyana cewa hakan ne kaɗai zai sa ma'aikata su samu sauƙi duba da kunci da wahalhalun rayuwar da aka shiga a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

People are also reading