Home Back

Hamas: Neman a matsawa Isra'ila amincewa da bukatocinsu

dw.com 2024/6/26

Wannan kira na Hamas na zuwa ne a yayin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ke karkare ziyarasa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kungiyar ta Hamas ta ce ta ji yadda Blinken ke magana a kan sabon kudirin yarjejeniyar da suka gabatar amma har yanzu basu ji komai daga bangaren Isra'ilaba.

Sakatare Blinken ya ce wasu daga cikin bukatun na Hamas za a iya amincewa da su amma dai masu shiga tsakani na kokarin ganin yadda za a cimma kyakyawar yarjejeniya.

Daga cikin sauye-sauyen da Hamas ta gabatar akwai bukatar sakin wasu Falasdinawa 100 da ke fuskantar zama kaso na shekaru a gidajen yarin Isra'ila.
 

People are also reading