Home Back

Senegal: Mafita ga Jamus kan masu neman mafaka

dw.com 2024/7/7
Jamus | Berlin | Olaf Scholz | Masu Neman Mafaka | Senegal | Ghana
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz

Wannan yunkurin na Berlin ya bi sahun matakin da gwamnatin Birtaniya da dauka na dogara ga Ruwanda, wajen fitar da bakin da ba a tantance hanyoyin neman mafakar da suka bi ba. Kasar Senegal da ke yammacin Afirka na sahun gaba, cikin hanyoyin da ke da hatsarin gaske da matasan Afirka ke amfani da su wajen shiga Turai ta barauniyar hanya. Amma hukumomin Jamus na son kasar ta zame musu cibiya ko sansani, na tsugunar da masu neman mafaka da ba a tantance takardunsu ba. Knut Gerschau dan majalisar dokokin Jamus ta Bundestag da aka zaba karkashin jam'iyyar FDP, ya ce suna lalube cikin duhu na kasashe uku a nahiyar Afirka da babu tashin hankali cikinsu domin kulla yarjejeniya da su ciki har da Senegal.

#b#Burin da gwamntin Jamus ta sa a gaba shi ne, samar da kasashen da za a yi amfani da su wajen bin diddigin takardu da dalilan bakin hauren da ke neman mafaka a Jamus. A cikin shekarar 2023 ga misali, sama da bakin haure dubu 320 ne suka mika takardun neman mafaka a kasar. Saboda haka ne jam'iyyar adawa mafi girma a Jamus, take neman dogara a kan yarjejeniyar hijira da Senegal da Ghana wajen cimma burin da ta sa a gaba, a cewar Thorsten Frei dan majalisar dokokin Jamus din ta Bundestag da aka zaba a karkashin jam'iyyar CDU: "Senegal da Ghana ,kasashe biyu ne da suke cikin jerin kasashen Afirka masu aminci. A dangane da haka daga mahangar Jamus babu wata fitina a can, kuma kasashe ne masu kwanciyar hankali da ake mutunta hakkin dan Adam."Sai dai dokar da ke hukunta masu neman jinsi da aka kafa a Ghana, na haifar da shakku a tsakanin masu fada a ji a Jamus. Ko da  gamayyar jam'iyyun da ke mulkin kasar na ganin cewar, akwai bukatar sara ana duban bakin gatari game da yarjejeniyar hijira da ake neman kullawa da Fadar Accra. Amma masu bincike kan lamuran da suka shafi hijira na kasa da kasa, na ganin cewar da walakin game da yukurin Jamus na tasa keyar bakin haure zuwa kasashen Afirka domin tantance su. Franck Düvell da ke bincike kan hijira a Jami'ar Osnabrück ya ce yarjejeniyar da gwamnatin Birtaniya ta kulla da Ruwanda ta zama abin misali. Yawancin kasashen Afirka, na fuskantar kalubale na miliyoyin 'yan gudun hijira da rikice-rikice ke shafa. Saboda haka ne wasu kwararru a fannin hijira ke ganin cewar dogaro a kansu wajen dakile kwararar bakin haure zai iya zama ihunka banza matukar kasashen na Turai ba su taimaka wajen magance matsalolin da ke haifar da hijirar ba.

People are also reading