Home Back

Abubuwa biyar da ke faruwa da tattalin arzikin China

bbc.com 2024/4/28

Asalin hoton, EPA

Three cargo ships sail on Huangpu River in China's financial centre Shanghai
Bayanan hoto, Kasuwar hannayen jari ta China ta karye a farkon shekarar nan

Tun daga lokacin da China ta yanke shawarar gyara da kuma faɗaɗa tattalin arzikinta a shekarar 1978, arzikinta na cikin gida ya dinga haɓaka da kashi 9 cikin 100 duk shekara a ma'auni na tsakatsaki.

Lokacin da annobar korona ta mamaye duniya, ta fuskanci ƙarancin bunƙasa na kashi 2.2 cikin 100 - mafi ƙanƙanta a tarihi - a 2020.

Arzikinta ya farfaɗo a shekara ta gaba zuwa kashi takwas, amma kuma ya ƙaru da kashi uku ne kacal a 2022.

Ko za a iya cewa China ta faɗa ƙangin rashin haɓakar tattalin arziki mafi tsawo?

Mun duba manyan batutuwa biyar a wannan maƙalar, waɗanda za su iya kasancewa dalilin da ya jawo wa tattalin arzikinta koma-baya, da kuma abin da hakan ke nufi ga sauran duniya.

1. Me ke faruwa da tattalin arzikin China?

A watan Janairu China ta sanar cewa tattalin arzikinta ya bunƙasa da kashi 5.2 cikin 100, na biyu a girma ke nan bayan na Indiya a cikin mafiya girman tattalin arziki na duniya a wajen habaka.

Tattalin arzikin China ya ninka na Indiya fiye da sau biyar a girma.

Amma a cikin ƙasar, mutane ba su gani a ƙasa ba; an samu kudaden zuba jari masu yawan gaske daga China zuwa wasu kasashe a 2023, karon farko ke nan cikin shekara biyar; rashin aikin yi tsakanin matasa ya kai ƙololuwa a tarihi zuwa kashi 20 cikin 100 a Yunin 2023; kuma kasuwar hannayen jari ta faɗi a farkon shekara.

A shekarar da ta wuce, wasu 'yan China da ransu ya baci sun nuna fushinsu a shafin ofishin jakadancin Amurka da ke China a dandalin Weibo.

Amma daga an goge mafi yawan saƙonnin, a cewar rahotonni.

Wani masanin tattalin arziki a bankin Dutch ING, Lynn Song, ya ce dalilin da ya sa tattalin arzikin China yake jan ƙafa wajen farfaɗowa tun bayan annobar korona shi ne "ba kamar sauran ƙasashe ba, China ba ta ɗauki tsauraran matakai ba da za su taimaka wa habakar arziƙin nata".

Ƙasashe kamar Amurka sun ƙaddamar da tsarin tallafin korona, inda ta ware dala tiriliyan 1.9 don taimaka wa marasa aikin yi da kuma masu ƙananan sana'o'i, da jihohi, da kuma ƙananan hukumomi.

Asalin hoton, Reuters

Da yawan 'yan China sun biya kuɗin gidajen da har yanzu ba a gina ba ko kuma ba a gama ba
Bayanan hoto, Da yawan 'yan China sun biya kuɗin gidajen da har yanzu ba a gina ba ko kuma ba a gama ba

Wang Tao ta bankin UBS ta bayyana ƙarin wani babban dalili da ya jawo ƙarancin habakar tattalin arzikin China. "China na cikin rikicin harkokin gine-gine mafi muni a tarihi.

"Sama da kashi 60 cikin 100 na arzikin 'yan ƙasa yana ɓangaren gine-gine ne. Idan farashin gidaje ya faɗo, to mutane suna ɗari-ɗarin kashe kuɗi, musamman ma masu tsakatsakin arziki. Misali shi ne, an rage sayen manyan kayayyakin amfani a gida," in ji ta.

2. Ko arzikin China zai zarta na Amurka?

Lokacin da China ta zama ta biyu mafi girman tattalin arziki a duniya a 2010, an yi ta hasashen zai iya zarta na Amurka.

Saboda an yi ta ganin yadda ƙasar ke faɗaɗa hanyoyin samunta a cikin gida; a shekara 20 kafin 2010, China ta samu haɓakar tattalin arzikin da ya zarta kashi 10 a karo biyu: 1992 zuwa 1995 da kuma 2003 zuwa 2007.

Kafin a samu tsaikon, hasashe mafi buri da yawa cewa China za ta zarta Amurka shi ne zuwa shekarar 2028, yayin da wasu suka hasaso 2032.

Amma ganin yadda ake fama da karayar tattalin arzikin a yanzu, ko China za ta iya yin hakan kuwa?

"E, amma dai ƙila ba nan kusa ba," in ji Farfesa Li Cheng, daraktan cibiyar Centre on Contemporary China and the World (CCCW) da ke jami'ar Hong Kong.

Shi kuwa Mista Xu ya ba da amsa da cewa: nan da shekarun 2040.

Cikin dalilan da Farfesa Li ya bayar akwai zaɓen shugaban ƙasa da Amurka za ta yi a shekarar nan, wanda zai haifar mata da rashin tabbas.

Ya ƙara da cewa, ita kuwa China ta samu ƙarin damarmaki kamar yadda take jagoranci a ɓangaren ƙera motoci masu amfani da lantarki, wanda hakan ya bai wa kowa mamaki.

3. Wane ƙalubale China za ta fuskanta?

Mista Song na ganin rashin ƙwarin gwiwa da mutane ke da shi na ƙara jawo ƙarancin zuba jari har da ma sayen kayayyaki, abin da ke jawo ƙarancin riba daga ƙarshe.

"Abin da zai taimaka shi ne kafa dokokin da za su tallafa wa tsaruka," in ji shi.

Wasu na fargabar Shugaban China Xi Jinping zai afka wa tsibirin Taiwan don yunƙurin daƙile bore.

China na ganin Taiwan mai ƙwarya-ƙwaryar 'yanci a matsayin yankinta da ya ɓalle kuma za ta dawo da shi.

Farfesa Mertha na ganin "indai ba ganganci ba - ina ganin za a ci gaba da nuna ƙarfin soji don jawo hankalin 'yan kishin ƙasa".

Farfesa Li ya yi gargaɗin cewa "duk wanda ke son yaƙi a Taiwan, ko dai mahukunta a China, ko Amurka, ko Taiwan, ya kamata su yi tunani sosai; wannan yaƙi ba zai zama iri ɗaya da na Ukraine ba".

"Wannan ne zai zama yaƙi na farko da za a yi ta hanyar ƙirƙirar basira. Za a yi fito-na-fito sosai da kayan fasaha, yaƙin nau'ra da na'ura."

4. Ta yaya jan ƙafar zai shafi tattalin arzikin duniya?

Mistra Xu na da ra'ayin cewa zai shafi duniya ta ɓangare uku: kayayyaki, yawon buɗe-ido a China, da kuma siyasar yankin.

"Na farko, tun a China ce babbar mai sayen kaya daga ƙasashen waje, idan ta kasa farfaɗowa za ta rage sayen kayayyakin, musamman waɗanda ake amfani da su a gine-gine kamar kuza da tama.

"Na biyu, janyewar 'yan China masu yawon buɗe-ido asara ce ga yankuna daban-daban - sashen yawon buɗe-ido zai daɗe bai dawo yadda yake ba kafin annobar korona.

"Na uku, jan ƙafa - musamman idan ya haɗu da ƙarancin arzikin ɗaiɗaikun mutane - zai daƙile yunƙurin China na mamaye siyasar duniya ta hanyar ba da tallafi da kuma rance."

Cikin shekara 10 da suka gabata, China ta ƙaddamar da shirin Belt and Road Initiative (BRI) don jaddada matsayinta a faɗin duniya ta hanyar zuba jari a manyan ayyukan raya ƙasa. Ta ƙulla yarjejeniya da ƙasashe 152 kuma ta zuba jari a ayyuka sama da 3,000.

Amma wasu masu suka sun ce shirin na BRI yana jawo "tarkon bashi" saboda yadda ƙasashe masu tasowa suke yawan neman bashi daga China ta cikin shirin.

5. China za ta iya farfaɗowa?

Mista Song na ganin ƙalubalen da ke gaban China shi ne cimma burinta na haɓakar tattalin arziki.

"Babban abu ga China shi ne ta mayar da hankali wajen magance rikici a ɓangaren gine-gine," a cewar Mista Xu.

"Abu ne biyu kuma, ta lura da abin da ake nema a cikin ƙasar, maimakon mayar da hankali kan ɓangaren sarrafa kayayyaki kawai."

A gefe guda kuma, Mista Song ya ce shugabannin China za su mayar da hankali kan cimma haɓakar kashi 5 cikin 100 na arzikin cikin gida atau GDP kamar yadda suka tsara.

"Duk da cewa mun ga irin sauye-sauyen manufofi kan tattalin arziki, har yanzu akwai buƙatar tsare-tsare nan da 'yan makonni ko watanni da za su taimaka wajen cimma burin da aka saka a gaba a 2024."

 
People are also reading