Innalillahi, Allah Ya Yiwa Wata Hajiya Daga Jihar Kaduna Rasuwa a Ƙasa Mai Tsarki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Saudi Arabia - Allah ya yi wa wata mahajjaciya daga jihar Kaduna, Hajiya Asma’u Muhammad-Ladan rasuwa a kasa mai tsarki.
Hajiya Asma'u ta rasu ne a asibitin King Fahad da ke birnin Makkah a Saudi Arabia ranar Jumu'a, 14 ga watan Yuni bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kaduna, Malam Yunusa Muhammad-Abdullahi ne ya bayyana haka a ranar hawan Arafah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sanarwar da ya rabawa manema labarai yau Asabar, Malam Yunusa bai bayyana sunan ƙaramar hukumar da marigayyar ta hito ba, Daily Trust ta ruwaito.
Ya ƙara da cewa Hajiya Asma'u ta yi rijista a hedkwatar hukumar alhazan kafin Allah ya karɓi rayuwarta.
Haka nan kuma mai magana da yawun hukumar alhazan Kaduna ya sanar da cewa tuni aka tura saƙon rasuwarta ga iyalanta.
Ya kara da cewa, mahukunta da ma’aikatan hukumar sun jajanta musu bisa rasuwar Hajiya Asma’u.
A cewar Muhamamda-Abdllajhi, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna ta yi addu’ar Allah SWT ya jikan marigayiyar, ya gafarta mata kuma ya bai wa iyalanta haƙuri.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da alhazai sama da miliyan 1.5 ke hawan Arafah, ɗaya daga cikin ranaku masu muhimmanci da falala a addinin Musulunci.
A wani rahoton kuma hukumar kula da Masallatai masu alfarma a ƙasa mai tsarki ta ce za a fassara hudubar hawan Arfah zuwa harshen Hausa da wasu harsuna 19.
Alhazai sama da miliyan 1.5 ne za su taru a filin Arafah ranar Asabar, 16 ga watan Yuni cikinsu har da Musulmi 65,000 daga Najeriya.
Asali: Legit.ng