Home Back

CMG Ya Yi Kyakkyawar Fita A Dandalin St. Petersburg Karo Na 27

leadership.ng 2024/9/27
CMG Ya Yi Kyakkyawar Fita A Dandalin St. Petersburg Karo Na 27

A bana ne ake bikin cika shekaru 75 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Rasha. A matsayin sa na kamfanin watsa labarai dake kawance da takwarorinsa na Rasha, CMG ya sake halartar dandalin kasa da kasa na harkokin tattalin arziki na St. Petersburg karo na 27, wanda ya gudana tsakanin ranaikun 5 zuwa 8 ga watan nan na Yuni, inda ya kafa sashen baje harkokinsa, mai fadin sakwaya mita 85, a babbar harabar gudanar da dandalin, wanda ya zamo wuri mafi girma da aka taba amfani da shi domin baje ayyukan taron a tarihi.

Yayin gudanar da dandalin, CMG ya yi amfani da tsare tsaren taron wajen yayata musaya, da hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labaran Sin da na Rasha, kana ya yi tattaunawa da wakilan kafar Gazprom mafi girma a fannin watsa labarai a Rasha. Sassan biyu sun tsara zurfafa hadin gwiwa, da hada karfi wajen fitar da shirye shiryen kafofin watsa labarai masu jigon biki, na cikar huldar diflomasiyyar kasashen biyu shekaru 75 da kafuwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

People are also reading