Home Back

Rikicin Masarautar Kano: Kotu Ta Sake Ɗage Shari’ar Zuwa 4 Ga Watan Yuli

leadership.ng 3 days ago
Rikicin Masarautar Kano: Kotu Ta Sake Ɗage Shari’ar Zuwa 4 Ga Watan Yuli

Wata babbar kotun jihar Kano, ta sanya ranar 4 ga watan Yuli, domin ci gaba sauraren ƙararrakin taƙaddamar masarautar Kano da ke gabanta kan Sarkin na 15, Aminu Ado-Bayero.

Masu shigar da ƙarar sun haɗa da Babban Lauyan Kano, da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar da kuma Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta hannun lauyansu, Ibrahim Isah-Wangida Esq, tun a ranar 27 ga Mayu, 2024, inda suke neman a hana Aminu Ado-Bayero da wasu sarakunan Bichi da Rano da Gaya da kuma Ƙaraye a matsayin Sarakuna.

Waɗanda ake ƙarar sune Alhaji Aminu Ado-Bayero da sauran sarakunan da sabuwar dokar ta tsige da kuma jami’an tsaron jihar Kano.

A lokacin da aka ci gaba da sauraren ƙarar a yau Talata, Lauyan masu shigar da ƙara, Eyitayo Fatogun, SAN, ya shaida wa kotun cewa an gabatar musu da saƙonni biyar a ranar 1 ga watan Yuli da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, inda ya buƙaci kotun da ta yi watsi da lamarin don ba su damar yi wa wadanda ake ƙara martani

Lauyan Aminu Ado Bayero, Abdul Muhammed, ya nuna rashin amincewa da wannan buƙata inda ya nemi a ɗage zaman domin su samo amsa da kuma shigar da dukkan bukatunsu, kana mai shari’a Amina Adamu-Aliyu, ta ɗage ci gaba da sauraren ƙarar har zuwa ranar 4 ga watan Yuli, 2024.

Idan ba a manta ba a ranar 27 ga watan Mayu, ne kotun ta bayar da umarnin dakatar da wanɗanda ake ƙara da su daina gabatar da kansu a matsayin sarakuna domin samun zaman lafiya a Kano.

People are also reading