Ana Shirin Shiga Yajin Aiki, Kungiyoyin Kwadago Sun Nemi Sabuwar Bukata Wajen Tinubu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyoyin ƙwadago sun yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya sa baki a tattaunawar da suke yi da gwamnatin tarayya kan sabon mafi ƙarancin albashi.
A cewar ƙungiyoyin, shiga tsakanin da Tinubu zai yi a tattaunawar na iya taimakawa wajen daƙile yajin aikin da aka shirya farawa a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni.
Wasu majiyoyi da dama a NLC da TUC sun bayyana cewa bai kamata gwamnatin tarayya da kamfanoni masu zaman kansu su yi tunanin cewa ma’aikata za su karɓi wani abu da bai kai gidan dubu ɗaruruwa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun koka da cewa tayin da gwamnati ta yi, ya yi kaɗan duba da yadda hauhawar farashin kayayyaki ke ƙara ƙamari.
A wata hira da jaridar The Punch, babban ma’ajin ƙungiyar NLC, Hakeem Ambali, ya buƙaci Tinubu da kansa ya sa baki a tattaunawar da ake yi kan mafi ƙarancin albashi.
Ya buƙaci ya kira dukkanin ɓangarorin da ke da alhaki a tattaunawar domin daƙile yajin aikin, yana mai jaddada cewa tayin N60,000 da gwamnatin tarayya ta yi ya yi kaɗan.
Hakeem Ambali, ya yi nuni da cewa Shugaba Tinubu zai iya hana yajin aikin idan shi da kansa ya sa baki a tattaunawar da ake yi da ƙungiyoyin ƙwadagon.
"A cikin sa’o’i 24, gwamnatin tarayya da shugaban ƙasa za su iya hana yajin aikin idan shi (Tinubu) ya nuna da gaske yake. Shi ne ke da ta cewa a kan komai."
- Hakeem Ambali
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta roƙi ƙungiyoyin ƙwadago kan shirinsu na shiga yajin aiki.
Gwamnatin ta buƙaci da su sake duba matakin da suka ɗauka na shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Litinin, 3 ga watan Yuni 2024.
Asali: Legit.ng