Sojoji Sun Kama Ɗan Ta’adda Yana Kokarin Guduwa Bayan Ya Kashe Mutane
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Taraba - Rundunar sojin Najeriya ta sanar da kama dan ta'addar da ya fitini yankuna da dama a jihar Taraba.
Rundunar ta ce ta kama dan ta'addar mai Suna Ibrahim Hassan ne yayin da yake kokarin tserewa bayan sun kai hari kan wasu mutane.
Legit ta tabbatar da haka ne a cikin sakon da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook a yau Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar sojin Najeriya ta ce ɗan ta'addar mai suna Ibrahim Hassan ya kai mummunan hari garin Mararaban Agazawa da ke jihar Taraba.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya jawo asarar rayuka biyar tare da jikkata mutane da dama da satar dukiya.
Rundunar sojin ta ce biyo bayan harin, cikin gaggawa ta tsunduma neman 'yan ta'addar a ranar 16 da watan Yuni.
Ana cikin haka ne rundunar ta cafke shugaban ƴan ta'addar da suka kai harin kuma ta kwato makamai a wajensa da babur da suka sace yayin harin.
Shugaban rundunar, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa ya ce ɗan ta'addar ya amsa laifin kai harin garin Mararaban Agazawa da sauran wurare a jihar Taraba.
Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa ya kuma tabbatar da cewa a yanzu haka ana cigaba da bincike domin daukan mataki na gaba kan ɗan ta'addar
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya taya hafsoshin tsaron Najeriya da sufetan yan sanda na kasa murna.
Ya ce yana da yaƙinin cewa suna da gogewar da zasu iya magance matsalar tsaron da ta addabi jihar Filato da yankunan Najeriya baki ɗaya.
Asali: Legit.ng