Home Back

Jirgin Sama Dauke Da Mataimakin Shugaban Kasar Malawi Ya Yi Batan-Dabo

leadership.ng 2024/7/3
Jirgin Sama Dauke Da Mataimakin Shugaban Kasar Malawi Ya Yi Batan-Dabo

Wani jirgin sama dauke da Mataimakin Shugaban Kasar Malawi, Saulos Chilima da wasu mutane tara ya yi batan dabo.

Sakataren Shugaban Kasar shugaban kasar, Colleen Zamba, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta bayyana cewar, an daina jin duriyar jirgin saman mallakin Ma’aikatar Tsaron Malawi bayan da ya bar babbar birnin kasar, lilonge, a ranar Litinin da safe.

Shugaban kasar ya bayar da umarnin gudanar da aikin ceto bayan da jami’an sufurin jiragen sama suka gaza jin duriyar jirgin.

Kamata yayi jirgin ya sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Mzuzu, da ke shiyyar arewacin kasar da misalin karfe 10 na safe.

Bayan da aka sanar da shi game da afkuwar lamarin, nan take shugaban kasar Lazarus Chakwera ya soke tafiyar da ya shirya yi zuwa tsibirin Bahamas.

A cewar sanarwar, “ofishin shugaban kasa da majalisar ministoci na sanar da al’umma cewar jirgin sama mallakin Ma’aikatar Tsaron Malawi da ya bar birnin Lilonge a ranar Litinin, 10 ga watan Yunin da muke ciki da misalin 9 da minti 17 na safe, dauke da mataimakin shugaban kasa, Klaus Chilima, da wasu mutane tara, ya gaza sauka a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Mzuzu da misalin karfe 10 na safiya kamar yadda aka tsara”.

Sanarwar ta ce za a yi wa al’ummar kasar karin haske da zarar hukumomi sun samu bayani game da jirgin.

People are also reading