Home Back

NEJA: Tsoron ‘yan bindiga ya hana ceto mutum 50 da ramin haƙar ma’adinai ya rufta da su – Hukumar Agaji

premiumtimesng.com 2024/6/18
Rundunar NSCDC ta kama mutum 8 da ma’adinai da suka hako ba bisa ka’ida ba a Kaduna

Rahotanni sun tabbatar da cewa har yanzu akwai ƙimanin mutum 50 da ke ƙarƙashin ƙasa, waɗanda ramin haƙar ma’adinai ya rufta da su, a yankin Galkogo, cikin Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja.

Wani kamfani ne mai suna “African Minerals and Industries Limited” ke aikin haƙar ma’adinai a yankin, inda wurin ya rufta bayan saukar ruwan sama mai ƙarfi, kuma ya turbuɗe ƙimanin mutun 50 a ƙarƙashin ƙasa.

Daga cikin waɗanda ramin ya rufta da su a ranar Lahadi, har da manajan kamfaninai suna Ibrahim Ishaku.

An kuma ji cewa wani mutum mai suna Kuta, wanda shi ne babban jami’in tsaro a wurin, ya haɗu da ajalin sa, yayin ƙoƙarin da ya yi ya ceto wasu da ramin ya rufta da su.

Daga baya an ceto mutum shida, waɗanda dukkan su sun ji raunuka, kuma aka garzaya da su wata cibiyar kula da lafiya a yankin.

An kuma ji cewa daga baya yayin da majiya ƙarfi suka taru ana aikin ceto wasu da ke ƙarƙashin ƙasar, sai wani gefe na ramin ya ƙara ruftawa, wanda hakan ya sa tilas masu aikin ceton tserewa a guje.

Har zuwa lokacin da ake rubuta wannan labari dai mutum 50 na can ƙarƙashin ƙasa, ba a san halin da su ke ciki ba. Hakan ya sa wasu na fargabar cewa sun ma rasa ran su a ƙarƙashin ƙasa.

Jami’in Hulɗa da Jama’a ma Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Hussaini Ibrahim, ya tabbatar da haka cikin wata sanarwar da ya fitar ranar Litinin, a Minna, babban birnin Jihar Neja.

Ya ce, “saboda yanayin dajin akwai ‘yan bindiga, ya sa ba a samun takamaimen labarin yanayin da ake ciki da wurin a halin yanzu. Ba za a ce an ceto ba har yanzu.”

Sai dai kuma ya ce an tura masu ceto domin su fito da su daga cikin ramun.

Ya kuma tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kai hari a yankuna biyu cikin Jihar Neja, a ranar Lahadi da dare.

Sun arce da mutum shida a ƙauyen Malam Adogo, cikin Ƙaramar Hukumar Mashegun, sannan a Turgar Kawo kuwa sun kwashi mutum kamar 20. A Mazaɓar Erena ta Ƙaramar Hukumar Shiroro kuwa, sun gudu da shanu ɗaruruwa.

People are also reading