Zargin Rashawa: Kotu Ta Ba EFCC Sabon Umarni Kan Yunƙurin Kama Rabiu Kwankwaso
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Wata babbar kotu a jihar Kano mai zamanta a cikin sakatariyar Audu Bako ta dakatar da hukumar EFCC daga gayyata, tuhuma, tsarewa ko hantarar Rabiu Musa Kwankwaso.
Jam'iyyar NNPP, Dr. Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Chif Clement Anele, Lady Folshade Aliu, Injiniya Buba Galadima da Sanata Rabiu Kwankwaso ne suka shigar da karar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa babbar kotun ta hana EFCC ta dauki wani mataki kan jagoran jam'iyyar NNPP da wasu mutane bakwai kan zargin da take yi masu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar da ke yaki da masu yi wa dukiyar al'uma zagon kasa (EFCC) kadai ake kara a shari'ar, kuma ita kadai aka hana ta tuhumi Kwankwaso a yanzu.
Mai shari'a Yusuf Ubale Muhammad ne ya ba da wannan umarnin na wucin gadi bayan da ya karanta bukatar da masu shigar da karar suka gabatar a ranar 5 ga watan Yunin 2024.
Mai shari'a Yusuf ya ce:
"Kotu ta ba da wannan umarnin ga wanda ake ƙara. Kotu ta haramta wa wanda ake kara, ko jami'anta, ko wakilanta daga kama wadanda suka shigar da karar.
"Kotun ta ba da umarni a kan ka da a kama, ko a tsare, ko a gayyaci wadanda ake kara ko a hantare su ko a muzguna masu, har sai an kammala wannan shari'ar."
Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Yunin 2024.
A wani labarin, mun ruwaito cewa jirgin sama dauke da mataimakin shugaban kasa (VP) na kasar Malawi, Saulos Klaus Chilima ya bace bat.
Wata sanarwa da ofishin shugaban kasa da ministocin Malawi ya fitar ta ce duk wani kokari na tuntubar jirgin ya ci tura amma ana kan nema.
Asali: Legit.ng