Home Back

Garambawul Da Muke Wa Tsarin Aikin Sojojin Nijeriya –Janar Musa

leadership.ng 2024/6/29
Garambawul Da Muke Wa Tsarin Aikin Sojojin Nijeriya –Janar Musa

Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Nijeriya, Janar Christopher Musa ya bayyana yadda a halin yanzu rundunar sojin Nijeriya take kokarin samar da walwala ga jami’anta domin dawo da su hayyacinsu da kuma yin garambawul a aikin soji.

Janar din ya bayyana haka ne a wata ganawa da manema labarai da ya yi a ofishinsa kwanan baya. Mun yi nazarin bidiyon tattaunawar daga kafar yada labarai ta DW.

Da aka tambaye shi irin sauyin da ya kawo tun lokacin da aka nada shi shugaban rundunonin sojin ruwa da sama da na kasa. Ya bayyana cewa, tun kafin zuwa wannan lokaci ya zauna a Maiduguri wajen watanni 19, “inda Allah ya taimake mu muka yi aiki a can kuma muka samar da hadin kan jama’a, kuma muka nusar da al’umma cewa kowa yana da aikin da ya kamata ya yi domin kawo zaman lafiya, kowa akwai gudunmawar da ya kamata ya rika kawowa, domin shi wannan aiki mu kadai ba za mu iya yi ba sai da taimakon jama’a, kuma yin hakan yana taimako sosai, shi ya sa a yanzu abubuwa suke canjawa.

 “Baya ga hakan, muna hulda da jama’a ba wai zaman ofis kawai muke yi ba muna fita waje muna hada kai da mutane da sauran ma’aikatu, muna gaya musu cewa ya kamata su ma su taimaka, domin duk wanda ya zo muka yi aiki tare muna yi ne don mu samu nasara,” in ji shi.

Da yake magana game da tsarin kula da walwalar sojojin da suke filin daga kuwa, Janar Musa ya ce, “Eh, mun sani cewa, idan soja ya ji dadin aikin da yake yi kuma yana samun abinci, albashinsa na zuwa ana taimakon iyalinsa da komai, to zai sa kwazo sosai domin ya samu nasara. To matakin dai da muka dauka yanzu shi ne, wadanda suka samu rauni a filin daga ana kai su asibiti ana lura da su yadda ya kamata, wadanda ma abin ya yi kamari ana kai su kasashen waje don su samu kulawa, wadanda kuma suka mutu ana tabbatar da cewa abubuwan da ya kamata a ba su na hakkinsu ana ba su, matansu gwamnati tana kula da su domin sun rasa mazajensu.”

Da ya koma kan batun kokarin da gwamnatin Shugaba Tinubu ke yi na samar da alawus din sojoji kuwa, cewa ya yi, “To na farko dai abin da ake ciki mun dai tabbatar cewa kowa yana samun albashinsa yadda ya kamata, alawus dinsa yana samuwa, kayayyakin da yake bukata na aiki da na sawa ana bayarwa. Eh, babu shakka kudin bai da yawa ba ya isa amma muna roka a kara musu kuma shi shugaban kasa ya yarda cewa gaskiya ya kamata a kara kuma ana kan aiki, ka san ba abin da za a yi a kwana daya ba ne, to abubuwan suna tafiya kuma sojojinmu suna aiki tsakaninsu da Allah kuma suna cewa shi shugaban kasa yana tare da su.”

Da ya zo magana kan sojojin da ake bari a filin daga na tsawon lokaci ba tare da sun ga iyalinsu ba, Janar Christopher Musa ya bayyana cewa, a halin yanzu suna tabbatar da kowane soja yana samun damar ya je ya ga iyalinsa ya dawo ta hanyar ba da ‘Pass’, sannan kuma bayan shekara daya ko shekara biyu ana canja su gaba daya, duk inda suke aiki ma ana samu a canja su kuma ana ba su lokaci su je su ga iyalinsu.

“Mu ma mun san cewa idan soja ya zauna bai ga iyali ba yana damuwa ba zai yi aiki yadda ya kamata ba, wannan abu ne da muka dauke shi da muhimmanci.

A can Borno muna da jirgin sama da yake daukar su sati bibiyu su je hutu su dawo, sannan haka muke yi a sauran wurare don aiki ya ci gaba,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, a kowane wata ana daukar sunaye, “mun san lokacin da ka zo don ba mu so ka dade da yawa, to abin da muke yi kenan kuma mun tabbatar da wannan tsarin yana aiki sosai.”

Dangane da batun hakkin sojojin da suka rasa rayukansu da aka ce aka rikewa kuwa, cewa ya yi “ai wannan a da kenan, amma a yanzu da zarar abin ya faru ake daukar mataki, za mu tabbatar sun samu hakkinsu don ba mu son su sha wahala.

“Ka ga wadanda suke da rai suna kallon wadanda suka rasu, idan ba su ga ana kyauta musu ba to babu wanda zai ba da kuzari wajen aiki. Wadanda suka rasu kwanaki da shugaban kasa ya je wajen jana’izarsu ka ga yadda ya ba wa ‘ya’yansu tallafin karatu ya kuma tabbatar da cewa za a biya su kudinsu tare da ba su gidaje, to abubuwanda ake yi kenan domin a tabbatar da cewa kasa na tare da su ba wanda za a manta da shi wai don ya rasu.

“Amma dama abin da muka gane shi ne, biyan alawus dinsu yana daukar lokaci, sai ka ga an yi shekara da shekaru ba a biya ba, amma mun yi magana da shugaban kasa yanzu ma ya ba da kudi ya ce a biya kowa gaba daya, to a halin yanzu abin da ake kan yi kenan za a biya su, ba ma son ana rike kudin kowa.”

A karshe ya ja hankalin masu aikata miyagun laifuka da ke kawo barazana ga zaman lafiyar kasa musamman ‘yan ta’adda da masu kai musu bayanai cewa su shiga taitayinsu.

“Abin da nake so na roki jama’a shi ne, mu sani wannan kasa da Allah ya ba mu kasa kuma mai albarka, dukkanmu mu hada kanmu domin ganin wannan kasar ta ci gaba, babu wanda zai iya wannan aiki shi kadai ko jami’an tsaro ko ‘yan siyasa dukkanmu ‘yan Nijeriya ya kamata mu kama aikin a yi tare, mu roki Allah, mu zauna mu tabbatar da cewa wannan kasa tamu ta ci gaba kuma tare ne za mu iya yi babu wanda zai iya yi shi kadai, kuma a bar hulda da ‘yan ta’adda, don muna da matsala da wadanda suke gaya musu ga sojoji nan, ga motoci nan, kaza-kaza-kaza, duk a bar wannan. Amma abin da nake fada a nan shi ne, abokin barawo barawo ne, mai aiki da ‘yan ta’adda shi ma dan ta’adda ne.”

People are also reading