Home Back

Mutane da Yawa Sun Mutu Yayin da Abubuwa Suka Fashe a Cikin Cunkosom Motoci

legit.ng 2024/5/10
  • Motoci aƙalla 100 ne suka ƙone yayin da wasu tankokin fetur suka fashe a cunkoson ababen hawa a titin Gabas-Yamna a Ribas
  • Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun maƙale a cikin motocinsu amma har yanzu ba a gano adadin da suka mutu ba
  • Gobarar ta shafe tsawon sa'o'i tana ci kafin daga bisani manyan motocin kashe wuta su samu nasarar shawo kan lamarin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Ana fargabar akalla motoci 100 da mutane masu yawa ne suka ƙone yayin da wasu tankokin fetur suka fashe a titin Gabas-Yamma a jihar Ribas.

Lamarin ya faru ne ranar Jumu'a, 26 ga watan Afrilu da daddare kuma ya kawo babban cikas ga matafiya a kan titin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Motocin kashe gobara.
An yi asara mai yawa yayin da tankoki suka fashe a cinkoso a jihar Ribas Hoto: Federal Fire Service Asali: Facebook

An tattaro cewa lamarin ya fara ne lokacin da wata tanka maƙare da man fetur ta fashe kuma ta kama da wuta kana ta bazu zuwa wasu tankokin da suka maƙale a cinkoso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma wutar ta bazu zuwa wasu motoci da suka maƙale a cunkoson kan titin, kuma har yanzu ba a san adadin yawan mutanen da suka mutu ba.

Yayin masu mutanen yankin suka ce motocu sama da 300 ne suka ƙone, wasu kuma sun bayyana cewa sun ƙirga akalla motoci 100 da suka ƙone.

Ko da yake ba a iya tantance adadin mutanen da abin ya rutsa da su ba, amma majiyoyi sun ce mutane da dama da ke cikin motocinsu ake fargabar wutar ta ƙone su.

Majiyoyin sun dora alhakin faruwar lamarin kan tukin ganganci da kuma kamfanin da ke gudanar da aikin sake gina sashin Eleme na titin.

An ce gobarar ta shafe sa’o’i da dama amma daga baya manyan motocin kashe gobara tare da tallafin kamfanin Indoroma Petrochemical ne suka kashe ta.

Asali: Legit.ng

People are also reading