Home Back

Kamfanin Kasar Sin Na Bayar Da Gudummawar Gani Wajen Bunkasa Kasar Najeriya

leadership.ng 2024/8/22
Kamfanin Kasar Sin Na Bayar Da Gudummawar Gani Wajen Bunkasa Kasar Najeriya

A ’yan kwanakin baya aka yi bikin komawar wasu matasa ’yan Najeriya gida, bayan da kamfanin gine-gine na CCECC na kasar Sin ya dauki nauyin kwasa-kwasan samun kwarewa da suka kammala a kasar Sin a fannin aikin injiniyan jiragen kasa, da sauran fannoni masu nasaba da harkokin sufuri, matakin da ya yi matukar samun yabo daga sassa da dama.

Wannan kwazo na kamfanin CCECC karkashin manufarsa ta tallafawa al’ummun dake wuraren da yake gudanar da ayyuka, ya nuna yadda kamfanonin kasar Sin masu gudanar da manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa ke sauke nauyin dake wuyansa na samar da ci gaba a duk inda suke ayyuka.

Kaza lika, wannan tallafi da kamfanin ya samar ga dalibai ’yan Najeriya ya yi daidai da burin gwamnatin kasar na kara yayata shigar matasa ’yan kasar cikin harkokin sufurin jiragen kasa, kamar yadda hakan ke kunshe cikin manufar raya layukan dogo a Najeriya wadda gwamnatin kasar ta kaddamar a shekarar 2018.

Kamar dai yadda muke gani a nan kasar Sin, fannin sufuri ta layukan dogo ya zamo babban ginshiki dake taka rawar gani a bangaren kyautata rayuwar al’umma ta fuskoki da dama, wadanda suka hada da saukaka farashi da hidimomin zirga-zirga, dakon manyan hajoji, samar da guraben ayyukan yi da haraji, da kyautata amfani da makamashi mai tsafta a fannin sufuri da dai sauransu. Hakan na nufin idan irin wadannan manufofi na hadin gwiwa da tallafi daga kasar Sin suka dore, Najeriya da ma sauran sassan kasa da kasa musamman kasashe masu tasowa, za su amfana matuka daga fasahohin zamani na ci gaban sufuri ta layukan dogo.

Yanzu haka dai Najeriya na kan hanyar aiwatar da manufofin zamanintar da harkokin sufuri ta layukan dogo na tsawon shekaru 25, kuma za a aiwatar da hakan ne ta hanyar horas da matasa da za su rika samun kwarewa a aikace, don haka masharhanta da dama ke jinjinawa kamfanin CCECC bisa gudummawar kai tsaye da ya baiwa wannan manufa.

Ko shakka babu CCECC ya cancanci yabo, kuma tallafin kwarewa da ya samarwa wadannan matasa ’yan Najeriya, ya kara tabbatar da aniyar kasar Sin ta ci gaba da bunkasa hadin gwiwar moriyar juna da bangaren Najeriya, yayin da sassan biyu ke kara himmatuwa wajen zurfafa fahimtar juna, da fadada alakarsu daga dukkanin fannoni.

People are also reading