Home Back

PDP Ta Watsawa Atiku Ƙasa a Ido Kan Hadaka da Kwankwaso, Obi, Ta Yi Alfahari

legit.ng 2024/7/1
  • Jam'iyyar PDP a Najeriya ta yi fatali da shirye-shiryen da Atiku Abubakar ke yi na haɗaka da sauran jam'iyyun adawa
  • Jam'iyyar ta ce babu wani shiri da take yi a kan haka sai dai kofofinta a bude suke ga duk mai sha'awar shigowa cikinta
  • Sakataren yada labaran jami'yyar, Debo Ologunagba shi ya tabbatar da haka a yau Laraba 5 ga watan Yuni bayan wata ganawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP ta yi martani kan jita-jitar haɗaka da sauran jam'iyyun adawa a Najeriya.

Jam'iyyar ta nesanta kanta da labarin inda ta ce babu wannan maganar amma kofa a bude take ga duk mai son shigowa.

PDP ta yi martani kan hadakar Atiku, Obi da Kwankwaso
Jami'yyar PDP ta musanta shirin haɗaka da jam'iyyun adawa a Najeriya. Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso, Peter Obi. Asali: Facebook

PDP ta bugi kirji kan karfinta a Najeriya

Wannnan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da sakataren yada labaran jami'yyar, Debo Ologunagba ya fitar a shafin Facebook a yau Laraba 5 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ologunagba ya bayyana yadda mutane ke tururuwa zuwa PDP inda ya ce hakan ya nuna jam'iyyar ce kadai zabin ƴan kasar a yanzu.

PDP ta ce kofofinta a bude suk

"Kwamitin gudanarwa na jam'iyya bayan ganawa ta 58 ya tabbatar da cewa PDP ba ta shirin haɗaka da jam'iyyun adawa."
"Sai dai ta ce a matsayin PDP na jam'iyyar al'umma, kofofinta a bude suke ga ƴan Najeriya da sauran mambobin da suka fice daga cikinta."
"PDP ta kasance jam'iyyar adawa mafi karfi wacce za ta iya cin zabe a Najeriya ba tare da magudi ba."

- Debo Ologunagba

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading