Home Back

Dala Biliyan 95! Shin Da Gaske Kasar Amurka Tana Da Karamci?

leadership.ng 2024/5/14
Dala Biliyan 95! Shin Da Gaske Kasar Amurka Tana Da Karamci?

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya sa hannu a kan wani shirin dokar samar da gudummawa ga kasashen ketare da ya kunshi dala biliyan 95, bayan da majalisun dokokin kasar suka zartas da shi. An ce, daga cikinsa, za a ware gudummawar da ta kai biliyan 60.8 ga Ukraine da ma biliyan 26 ga Isra’ila, baya ga dala biliyan 8 da za a samar ga yankin Asiya da tekun Pasifik da sunan wai tabbatar da“tsaron yankin Indo-Pasifik”. Daga nan kuma, shirin dokar ya fara aiki a hukumance. Bayan da ya sa hannu a dokar, shugaba Biden ya bayyana cewa, za a fara jigilar makamai da kudinsu ya kai dala biliyan daya zuwa Ukraine cikin wasu sa’o’i kadan. 

Da yake amsa tambayoyin manema labarai game da zartas da shirin dokar da aka yi, shugaban majalisar wakilai ta kasar Amurka, Mike Johnson ya bayyana cewa, “Babu kwanciyar hankali a duniyarmu, wadda tamkar ma’ajiyar albarusai ce, don haka muka yi kokari, kuma ina ganin tarihi zai ba da amsa.” To, amma ko da gaske ne abin haka yake kamar yadda ‘yan siyasar Amurka irinsu Mr. Mike Johnson suka fada?

Babu shakka, duniyarmu na fama da tashe-tashen hankali. Rikici na ci gaba a tsakanin Rasha da Ukraine sama da shekaru biyu bayan barkewarsa, ga kuma tabarbarewar rikici a tsakanin Palasdinu da Isra’ila, wanda har ya haifar da mummunan tasiri ga sauran kasashen shiyyar. Yake-yake sun haifar da munanan hasarorin rayuka da kuma matsalolin jin kai. A kan ce, babu wanda ya ci nasara a fagen yaki. Amma bayan fagen yaki, akwai kasar da ke cin kazamar riba. Bisa kididdigar da aka samar, an ce, gudummawar da Amurka ta samar wa Ukraine ta kai dala biliyan 43.7 tun bayan barkewar rikicin a shekarar 2022, sai kuma a watan Nuwamban bara, majalisun dokokin Amurka sun amince da samar da gudummawar soja da ta kai dala biliyan 14.3 ga Isra’ila. Amma a hakika, duk da cewa gudummawa ce ga kasashen ketare, amma akasarin kudaden sun shiga aljihun masu sayar da makamai na kasar ta Amurka ne. A wannan karo ma, daga cikin dala biliyan 60.8 da ta samar wa Ukraine, akwai dala biliyan 27.6 da aka ware musamman domin sayen makamai da tsarin kandagarkin makamai daga Amurka, kwatankwacin dala biliyan 9 ne kawai da aka ware wajen samar da gudummawar jin kai da farfado da tattalin arziki a kasar Ukraine.

Abin lura kuma shi ne, shirin dokar ta kuma tsara samar da dala biliyan 8.12 don “tinkarar matakan da babban yankin kasar Sin za ta dauka a yankin Indo-Pasifik”. Daga cikinsu kuwa, an ware dala biliyan 1.9 don samar da kayayyakin tsaro da ma hidimomi ga yankin Taiwan da ma sauran kawayen kasar Amurka da ke yankin. Babu shakka, hakan ya saba wa sanarwoyi guda uku da kasashen Sin da Amurka suka bayar cikin hadin gwiwa, kuma katsalanda ce a cikin harkokin gidan kasar Sin, wanda kuma ya isar da sakon da bai dace ba ga mahukuntan yankin Taiwan tare da tona mana asirin Amurka game da mugun burin da take son cimmawa a yankin Asiya da tekun Pasifik. Lallai Amurka ta yi ta kalubalantar kasar Sin a kan batun Taiwan da tekun kudancin kasar Sin, don tsananta sabani a yankin, ta yadda mahukuntan yankin Taiwan da ma sauran “kawayenta” na yankin za su ba ta hadin kai wajen cimma burinta.

Amurka na daukar kanta a matsayin kasar da ta fi samar da gudummawa ga kasashen ketare. Amma a hakika, kullum tana samar da gudummawa ce don habaka cimma moriyarta da kiyaye babakeren da ta kafa a duniya, wadda ta haifar da mummunan tasiri ga zaman lafiya da ci gaba a duniya.

Kamar yadda Mr.Mike Johnson ya fada, “Babu kwanciyar hankali a duniya, wadda tamkar ma’ajiyar albarusai ce.” Sai dai abin da Amurka ke yi na cinna wuta ga albarusan. Gudummawar nan ta dala biliyan 95, ta sake shaida wa duniya ainihin abin da ke kunshe a cikin gudummawar da Amurka ke samarwa duniya.(Mai Zane:Mustapha Bulama)

People are also reading