Home Back

Rikicin Manoma da Makiyaya Ya Barke a Jigawa, An Raunata Mutum 5

legit.ng 2024/6/28
  • Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa an samu ɓarkewar rikicin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta jihar
  • Kakakin rundunar ƴan sandan ya ce an raunata mutum biyar a rikicin da ya auku a dajin Hayin Kogi na ƙaramar hukumar
  • Ya bayyana cewa mutanen da suka samu raunukan an duba lafiyarsu a asibiti kuma ana ci gaba da ƙoƙarin cafko Fulanin da ake zargi da kai musu hari

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - An jikkata wasu manoma bayan barƙewar rikicin manoma da makiyaya a jihar Jigawa.

Rikicin dai ya ɓarke a tsakanin manoma da Fulani makiyaya a dajin Hayin Kogi cikin ƙaramar hukumar Birnin Kudu a jihar.

An raunata mutum biyar a Jigawa
Mutum biyar sun raunata a rikicin manoma da makiyaya a Jigawa Hoto: @PoliceNG Asali: Twitter

Rikicin manoma da makiyaya a Jigawa

Jaridar The Nation ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu ya fitar a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Rahoton da rundunar ƴan sanda ta samu ya bayyana cewa da misalin ƙarfe 2:00 na rana, wasu makiyaya na rugar Waza sun farmaki wasu manoma a dajin Hayin Kogi a ƙaramar hukumar Birnin Kudu."
"Manoman suna aikin gyara gonakinsu ne domin shirye-shiryen noman damina."
"A sakamakon hakan, wasu daga cikin manoman sun tsere tare da barin babur mai ƙafa uku, wayoyi da kayan aikin gona."

- DSP Lawan Shiisu

Mutum nawa aka raunata?

Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa bayan samun rahoton, an tura jami'an ƴan sanda da ke makwabtaka da dajin zuwa wurin da lamarin ya auku.

Ya bayyana cewa wani mutum mai shekara 42 tare da wasu mutum huɗu sun samu raunuka sannan an kai su babban asibitin Dutse, inda aka duba lafiyarsu sannan aka sallame su, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Ya yi bayanin cewa ana ci gaba da ƙoƙari domin cafke waɗanda ake zargin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Makiyayi ya datse hannun manomi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani makiyayi ya kai hari kan manoma a gonarsu a yankin Damakasuwa dake ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

A yayin afkawar da makiyayin mai suna Huzaifa Salisu ya yi wa manomin mai suna Bitrus Chawai ya yanke masa hannu da adda.

Asali: Legit.ng

People are also reading